Kungiyar NLC ta janye yajin aki a Najeriya
May 22, 2016Talla
Daga cikin dalilan da ya kai NLC ga daukar wannan mataki, har da ganawa da daya daga cikin kusoshin jam'iyyar APC da ke mulki Bola Tinubu, wanda ya ba ta tabbacin tattaunawa da gwamnatin Najeriya kan janye tallafin man fetur.
Amma kungiyar kwadagon ta ce za ta ci gaba da tattauna ne kan matsayinta na cewa mai ya koma kan Naira 86 da Kobo 40 kowane lita, maimakon Naira 145. Amma za ta tattauna ne ba tare da yajin aiki ba.
Babu wani alkawari da NLC ta samu daga gwamnatin Buhari kan yanje tallafin man fetur. Sai dai wannan yajin aiki bai samu karbuwa ba a Najeriya.