1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

KUNGIYAR PLOLISARIO TA SAKO FURSINOIN YAKIN ALJERIA 300

JAMILU SANINovember 7, 2003
https://p.dw.com/p/Bvnk

A kasar Aljeria shugaban kungiyar kwatar yancin yankin yammacin sahara ta Polisario,Muhamed Abdulazizi ya bada sanarwar zasu sako fursinonin yakin Morocco 300 da aka tsare a Aljeria tun zamanin yakin 1975 zuwa 1991. Wanan batu dai na sakin fursononin yakin Morooco da yan kungiyar kwatar yancin yammacin sahara suka ce zasu yi ya biyo bayan kiran da shugaban kasar Libya Muammar Gadafi yayi musu,da kuma shigowar watan Ramadan mai alfarma. Shugban dai na kungiyar Polisario dake yakin neman yancin kai daga kasar Morocco,wace kuma ke samun goyon bayan kasar Aljeria,ya baiyana cewa yau juma'a ake sa ran sako Fursinonin yakin na Morocco dake tsare a hanun su. Koda yake har kawo yanzu kungiyar kwatar yancin ta yammacin sahara na cigaba da tsare fursinonin yakin Morocco har 600,a hedakwatar su dake Tindour dake kudu maso yammacin Aljeria,kuma suna masu marhabin da jami'an dilomaciya na kasahen duniya da zasu kasance masu shiga tsakani ko hakan ya taimaka wajen kawo karshen rikicin da yaki ci yaki cinyewa na yammacin sahara. Tuni dai kasahen duniya suka bukaci gwamnatin kasar Aljeria dake talafawa kungiyar Polisario a yakin da take yi da kasar Morocco,data tabatar da ganin an sami masalaha ta sulhu a yakin yammacin sahara. Makoni biyu da suka gabata ne dai baban sakataren majalisar dikin duniya Kofi Anan ya baiyana cewa har kawo na fusakantar koma baya a batun sasanta rikicin yammacin sahara,wanda don haka ne ma ya bukaci Morocco data amince da kudirorin da majalisar dinkin duniya ta cimma na zaman lafiyar yakin yammacin sahara. Gwamnatin dai ta birnin Rabat ta fito fili ta nuna rashin amincewar ta da kudirorin majalisar dikin duniya,saboda a cewarta ta rigaya ta baiwa alumomin dake zaune a yammacin na sahara damar gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a,ko suna so a basu yancin kann su.
Tun bayan da aka amince a gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da makomar ta yammacin sahara ya sanya,kungiyar kwatar yancin yammacin sahara ta Polisario ta amince da batun tsagaita wuta,tun bayan da majaliasar dikin duniya ta shiga tsakani a shekara ta 1991.
shugban dai na kungiyar Polisarion Abdulaziz ya furta batun sakin fursinonin yakin Morocco ne,a lokacin da ya gudanar da wani taro na manema labaru a kusa da garin Aljiers shi da Seif Al Islam Al Gaddafi dan shugaban kasar Libya. Tun da farko dai sai da manzon musanman din na shugaban kasar Libya ga kungiyar Polisrio ya gana da shugban kasar Aljeria Abdulaziz Bouteflik. Tuni dai majalisar dikin duniya ta bukaci kungiyar Polisario ta sako fursononin yakin Morocco dake tsare a hanun su tun 1991. Da dama dai daga cikin fursinonin yakin na Moroco sun shafe shekaru 20 suna tsare a hedkwatar kungiyar Polisario dake Tindouf. A karo na farko cikin shekarun 1995,kungiyar ta Polisario ta sako fursinonin yakin Morocco,wanda kuma tuni fursinonin yakin na Morocco 243 suka isa gida tun watan Agustan da ya gabata.
Tun shekara ta 1973 kungiyar kwatar yancin yammacin sahara ta fara daukar makamai,don ganin sun kawo karshen mulkin kasahen Spain da Morocco a yankin na yammacin sahara.