Kungiyar SADC ta cika shekaru 25
August 18, 2017Kasar Afrika ta Kudu na shirin karbar ragamar shugabancin kugiyar bunkasa tattalin arziki ta kasashen gabashin Afirka SADC a taron kungiyar da za a yi a birnin Pretoriya a ranar Asabar 19 ga wannan wata na Agusta, wanda shugaba Jacob Zuma zai karbi jagorancin kungiyar daga Sarki Mswati na Swaziland. Ana sa ran shugaban na Afirka ta Kudu ya taka muhimiyar rawa a cikin kungiyar mai manbobi 15. Matsayin Afrika ta Kudu a cikin kungiyar, na da matsaloli, sakamakon yadda kasar ke daukar kanta a matsayin babbar yaya wadda kuma ke yin kaffa-kaffa wajen shiga cikin harkokin kasashen kungiyar wacce kuma ba ta shiga cikin kungiyar cinakayyar da ba mara shinge ba wada ta hada kasashen Swaziland da Bostwana da Lesotho da kuma kasar Namibiya.
Manufofin kungiyar bayan samar da ita.
Manufofin kungiyar wacce aka kafa ta 1992 a birnin Windoek na kasar Namibiya, su ne samar da zaman lafiya da jagoranci na kwarai a tsakanin kasahen da kuma huldar tattain arziki. A shekara ta 2008 kungiyar ta SADC ta cimma wata yarjejeniya cinikayya mara shinge, sai dai wasu kasashen ba su shiga ba saboda sun kauracewa yarjejeniyar, abin da ya sa har yanzu ci gaban da aka samu a cikin wasu kasashen kalilan ne, a cewar masharhanta. A cewarsu karara ta ke, ba a tsamanin kungiyar SADC za ta kasance ginshiki a fannin huldar kasuwanci marasa shingen tsakanin kasahen yankin a cikin lokaci kankani.
A farkon shekarun 1980 da aka girka kungiyar mai kama a haka wacce daga baya aka canza wa sunan manyan manufofinta a lokacin su ne na yaki da wariyar laubnin fata a Afrika ta Kudu ta fannin kasuwanci wanda Afrika ta Kudu ta yi wa kasahen yankin fnitikau kuma fafutukar da sukayi ta ita ce ta rashin yin dogaro da Afrika ta Kudu. Babu shakka kungiyar ta SADC ta sha faman ganin an nemi hanyoyin tattaunawa da samun sulhu a Zimbabuwe domin kawo sauyi amma ba tare da cimma nasara ba, sannan wani abin da za a iya cewa nasara ce, shi ne rawar da kungiyar ta taka wajen hana juyin mulki a kasar Lesotho a shekarar 2014. Sai kuma a kasar Madagaska, inda can ma kungiyar ta taka rawa wajen warware rikicin siyasar kasar a shekara ta 2009.