1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Taraiyar Turai tana duba yiwuwar lakabawa kasar Belarus takunkumi

March 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4X

Kungiyar Taraiyar Turai tana duba yiwuwar lakabawa kasar Belarus Takunkumi,biyowa bayan samun nasarar shugaba dake mulki Alexander Lukashenko.

Komishinar hulda da waje ta kungiyar Benita ferraro tayi gargadin cewa,mai yiwuwa ne a dauki mataki akan belarus ciki har da hana takardun visa ga jamian gwamnati.

Yanzu haka ministocin harkokin wajen Turai suna ganawa a birnin Brussels domin tattauna irin mataki da zasu dauka akan belarus.

A can birnin Minsk,hukumar zabe ta Belarus tace Lukashenko ya lashe kashi 82 da digo 6 cikin dari na kuriu da aka kada,abokin hamaiyarsa na kusa Alexander Milinkevich kashi 6 cikin dari.

Shugabannin adawan dai sun zargi gwamnati da laifin magudi da aringizon kuriu,Lukashenko a nashi bangare yace wannan zargi ba shi da tushe.