1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Taraiyar Turai tayi tayin ihsani ga Iran

Hauwa Abubakar AjejeMay 16, 2006

Kungiyar taraiyar Turai tace a shirye take ta bada taimakon fasahar nukiliya na zamani domin anfanin cikin gida ga Iran,idan har ta amince ta dakatar da shirinta na nukiliya,sai dai Iran din tayi watsi da wannan batu.

https://p.dw.com/p/Bu04
Hoto: dpa

Kungiyar ta taraiyar turai tayi tayin yiwa Iran wani ihsani na musamman domin ta dakatar da aiyukanta na nukiliya wanda kasashen yammacin duniya suke zaton na kera makaman kare dangi ne.

Mai kula da manufofin waje na kungiyar,Javier Solana,wajen taron kungiyar ya baiyana cewa,sunyi alkawarin baiwa Iran din taimakon fasaha mafi ingancin na zamani.

Kodayake baiyi wani karin bayani ba,amma yace tayin na kungiyar taraiyar turai wanda take fatar mikawa a karshen wannan wata,ya wuce tayinta na farko a fannonin fasaha,tattalin arziki da siyasa da Iran din tayi watsi da su a watan agustan bara.

Jamian diplomasiya dai sunce,ainihin tayin ya hada da cewa,kanfanonin kasahen yammaci zasu ginawa Iran tashoshin nukiliya tare kuma da samara mata da mai.

Kasashe 25 membobin komitin sulhu cikin wata sanarwar hadin gwiwa,sun baiyana cewa,sharadi guda na samun wannan taimako kuwa shine,Iran ta amince da dakatar da duk wasu aiyukan da suka shafi inganta sinadarin uraniyum,ciki kuwa har da bincike da sarrafa uraniyum din.

Tun kafin wannan tayin kuwa shugaban kasar Iran Mahmud Ahmedinajad ya rigaya ya kawadda batun amincewa da irin wannan tayi,a ranar lahadi data gabata.

A ranar litinin ministan harkokin wajen Iran Manucher Motaki,ya fadawa jakadun kasashen Burtaniya da Faransa da Jamus cewa,duk wata bukata ta dakatarwa ko jingine inganta uraniyum bai ma taso ba,kuma babu ko shakka ba zai samu karbuwa ba.

Kasar Amurka dai ta amince bisa manufa,wannan tayi na kungiyar taraiyar turai muddin dai ya kunshi batun lakabawa Iran din takunkumi idan taki dakatar da inganta sinadarin na uraniyum.

Sanarwar ta kungiyar EU ta amince da yancin Iran nayin anfani da makamashin nukiliya saboda anfaninta na gida,amma tace kungiyar ta turai ta amince gabaki dayansa,kudirin majalisar dinkin wanda zai tilasatawa Iran dakatar da inganta makamashin nukiliya.

Damuwa da kasashen yammacin duniya suke ci gaba dayi shine cewa,kusan tsawon shekaru 10 Iran ta boye shirinta na binciken nukiliya ga kasashen duniya.

Sakatare janar na majalisar dinkin duniya dai Kofi Annan,da yayi kira a gaggauta kawo karshen wannan rikici,yace,ya gamsu da ci gaba da bin hanyar diplomasiya wajen magance batun.

Kasar Sin a nata bangare,tace tana goyon bayan wannan tayi na kungiyar EU,sai dai dukkaninsu Sin da Rasha sunce basa goyon bayan wani batu na yin anfani da karfin soji akan kasar ta Iran.

Iran din a yau talata dai taci gaba da hakikancewa zata ci gaba da inganta uraniyum saboda tana da yancin yin hakan.

Kakakin maaikatar harkokin wajen Iran Hamid Reza Asefi,yace bai kamata tayin na kungiyar taraiyar turai ya shafi yancin Iran,kamar yadda yake kunshe cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ba.