1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar tarayyar Turai da rikicin nukiliyar

May 16, 2006
https://p.dw.com/p/BuyF

Kungiyar tarayyar turai ta yi alkawarin taimakawa Iran samar da makamashi na lumana domin kawo karshen dambarwa a game da rikicin nukiliyar kasar. Jamiín tsare tsaren harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Javier Solana, yace kungiyar tarayyar turan zata baiwa Iran fasahar kere kere mafi inganci domin taimaka mata cimma bukatar samar da hasken wutar lantarki ga alúmar ta. Yana mai cewa za su gabatar wa Iran jadawali ingantacce ta aiwatar da wannan shiri. Javier Solana ya kara da cewa bisa hadin gwiwa tsakanin kungiyar tarayyar turai da da sauran alúmomi na kasa da kasa za su taimakawa Iran idan tana son kafa tashar nukiliya ta samar da hasken wutar lantarki. A waje guda Iran ta jaddada kudirin cewa ba zata amince da dukkan wata shawara ko kuma tayi daga kungiyar turan ba matukar ya hada da bukatar dakatar da shirin ta na bunkasa sinadarin Uranium.