1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Tariyar Turai ta bada euro miliyan 40 ga Darfur

Hauwa Abubakar AjejeOctober 2, 2006

Kungiyar taraiayar turai ta bada taimakon ne don taimakon jamaa a yankin darfur,a lokacin wata ziyarar kwanaki biyu da tawagar kungiyar ta kai zuwa kasar Sudan .

https://p.dw.com/p/Btxw
Hoto: dpa

Tawagar karkashin shugaban kungiyar taraiyar turai Jose Emanuel Barroso ta kai wannan ziyara ce saboda samo hanyoyin da zaa kawo karshen tashe tashen hankula da halin da jamaar Darfur suke ciki,hanyoyi kuma da zasu samu karbuwa ga gwamnatin Sudan da kuma sauran kasashen duniya.

Kokarin da akeyi na janyo hankalin shugaban kasar Sudan Omar al Bashir ya amince da aikewa da dakarun Majalisar Dinkin Duniya 20,000 ya tsaya cik.

Kasashen yammacin duniya dai sun hakikance cewa dole ne Sudan ta sake duba wannan batu na aikewa da sojin na MDD,inda cikin makon daya gabata sakatariyar harkokin wajen Amurka Condi Rice tace dole ne Sudan ta amince da hakan ko kuma ta fuskanci fushin kasa da kasa.

Ana shi bangare shugaban kungiyar taraiyar turai yace ya kamata kasashen yammacin duniya su fuskanci gaskiyar cewa al Bashir yaki amincewa da kasancewar sojin na MDD,saboda haka a cewarsa ya zama wajibi su nemo hanyoyi da suka dace kafin waadin aikin dakarun kungiyar taraiyar Afrika da zai kare a ranar 31 ga watan disamba.

Al Bashir ya sake jaddada wannan kin amincewa tasa a karshen mako yana mai cewa wata boyayar ajanda ce ta Amurka.

Sai dai barroso yace yayi imanin cewa alBashir ya gane cewa halin da ake ciki yanzu ba zai dore ba,da kuma kara rage matsayin sudan a idanun kasashen duniya idan taci gaba da kin amincewar.

Maaikatan agaji da masu nazarin abubuwa da ke kai su komo sun baiyana cewa tashe tashen hankula a Darfur sai kara muni suke yitun bayan yarjejeniyar watan mayu tsakanin gwamnati da daya daga cikin kungiyoyin yan tawaye na yankin.

Amma gwamnan arewacin Darfur Yousif kabir yace halin da ake ciki ya inganta kuma basu bukatar sojin kasa da kasa,saboda haka a cewarsa jamaarsu basa maraba da sojin na MDD.

Wani maaikacin agaji Patrick Andrey yace halin da ake ciki abin damuwa ne,musamman ma a yankunan karkara,inda ake ganin cewa cikin wannan shekara da kyar ne manoma su samu kaiwa ga gonakinsu saboda halin da tsaron yankin yake ciki.