1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar ´yan´uwa musulmi a Masar ta musanta aukuwar kisan kiyashi

December 23, 2005
https://p.dw.com/p/BvFP
Kwanaki kalilan bayan da shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nijad ya karyata kisan kiyashin da aka yiwa yahudawa, babbar kungiyar ´yan adawa a Masar wato ta ´yan´uwa musulmi ta bayamna kisan kiyashi na yakin duniya na biyu da cewa almara ce kawai. A cikin wani sharhi da ya rubuta ta intanat, Shugaban kungiyar Mohammed Mehdi Akef ya ce da ma kasashen yamma na kai hari ga wadanda ke gaba da Isra´ila. Akef ya ba da misali da wani dan Birtaniya da ke karyata aukuwar kisan kiyashi wato David Irvin da kuma mawallafin kasar Faransa Roger Garoudy, wanda ake yanke hukunci a gidan maza a shekarar 1998 bayan ya saka ayar tambaya game da yiwa yahudawa kisan kare dangi. A halin da ake ciki kungiyar ta ´yan´uwa musulmi ita ce babbar ´yar adawa a majalisar dokokin kasar Masar.