1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyoyi sun soki kisan 'yan Shia a Najeriya

November 15, 2016

A Najeriya kungiyoyin kare hakin jama’a sun yi gargadi kan hatsarin da ke tattare da ci gaba da rasa rayyuka a duk lokacin da aka samu arangama tsakanin jami’an tsaro da ‘yan Shi’a abin da ke zama hatsari ga demmokradiya

https://p.dw.com/p/2SkGy
Nigeria Schiitische Muslime in Dakasoye
Hoto: A. Abubakar/AFP/Getty Images

Ssau bakwai kenan a jere ana fuskantar arangama a tsakanin jami’an tsaron Najeriyar da ‘yan Shi’a tun daga wanda ya samo asali a garin Zaria a ranar 12 ga watan Disambar 2015, lokacin da suka toshe hanya ga babban hafsan sojan Najeriya.

Kusan kowane lokaci aka fuskanci fito na fito tsakanin jami’an tsaron da ‘yan Shi’a lamarin na karewa da zub da jini da asarar rayuka. Na baya-bayan nan da ya faru a ranar Litinin a  Kano, inda aka kashe ‘yan Shi’a sama da goma, abin da ya sanya kungiyoyin kare hakkin jama’a nuna damuwa a kan abinda suka kira mai hatsari ga yanayin zamantakewar Najeriyar. Dr Kole Shattima jigo ne a kungiyoyin kare hakin jama’ar Najeriyar wanda ya soke matakin na kiasan yan Shi'a.

Koda yake ana hangen bari na bari ya kowace fitina to sai dai, ga ‘yayan Shi’a na ganin suna da ikon yin tattaki da ma gudanar da ibadar su, kamar yadda sauran al’ummar kasar ke yi. Amma kwararru a harkar yanayin zamantakewa na masu kashedin kokari na wuce iyaka.

Tuni dai har ta kai ga wasu matasa sun fara bin sahu ko kuwa koyi da abubuwan da ke faruwa, na daukan hukunci a hannu ta hanyar afkawa masu bin wannan tafarki na Shi'a, abin da Dr Kole Shattima yace akwai bukatar gwamnati ta hanzarta daukan mataki na gyara tun kafin lamarin ya lalace.

Al’umma Najeriya dai da cike da fata ta kaiwa ga kawo karshen zubar da jini, a dalilin rashin jituwa a tsakanin mabiya addinai da jami’an tsaro. Wanda kwararru suke bayyana cewa abu ne da za’a iya kaucewa zubar da jini da ma kashe rayyukan jama’a, musamman a daidai lokacin da Najeriya ke fama da rikici na Boko Haram da ke haifar da mummunar illa ga daukacin Najeriyar.