1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyyar Eu ta kara gargadin kasar Iran

March 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5Z

Kungiyyar gamayyar turai wato Eu, ta bukaci kasar Iran ta dakatar da sarrafa sanadarin ta na Uranium ko kuma ta fuskanci fushin Mdd.

Wannan dai bayanin na kunshe ne a cikin jawabin da kungiyyar ta gabatar a lokacin taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da yanzu haka keci gaba da gudana a birnin Vienna.

Ya zuwa yanzu dai tuni shugaban kasar ta Iran wato Mahmud Ahmadinajad ya mayar da martanin cewa babu gudu babu jada baya a game da wannan mataki da Iran ta dauka naci gaba da sarrafa sanadarin nata na Uranium.

A dai jiya talata ne mahukuntan Amurka da Russia suka yi watsi da matakin da kasar Iran ta gabatar na kyale ta ci gaba da sarrafa dan kankanin sanadarin na Uranium a cikin kasar tata.

Daga dai tun lokacin da ake wannan takaddama kawo yanzu, kasar ta Iran ta dage akan cewa Nukiliyarta ta kwanciyar hankali ce amma bata tashin zaune tsaye ba kamar yadda kasashen yamma ke zato.