1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyyar tsaro ta Nato ta aiwatar da sabon kuduri

December 8, 2005
https://p.dw.com/p/BvHO

Kungiyyar gamayyar Turai, wato Eu da kungiyyar Tsaro ta Nato sun yawaba sakatariyar harkokin wajen Amurka, wato Condoleeza Rice game da kalaman ta akan aiyukan hukumar leken asiri ta Amurka a nahiyar Turai.

Wannan yabo yazo ne jim kadan bayan Rice ta gabatar da jawabi a gaban taron kolin kungiyyar ta Eu da kuma ministocin harkokin wajen tsaro na kungiyyar ta Nato a can birnin Brussels na kasar Belgium.

Idan dai za a iya tunawa kafafen yada labaru sun bayar da rahoton cewa hukumar ta CIA nada wasu asirtattun gurare na azabtar da fursunoni a wasu kasashe na gabashin Turai, kuma Jamus na daga cikin kasashen da ake amfani da wasu filayen jiragen samar kasar wajen jigilar fursunonin izuwa ire iren wadan nan gurare.

Bugu da kari, ministocin harkokin wajen da kasashen su ke cikin kungiyyar ta Nato sun amince da fadada aiyukan kungiyyar a can kasar Afhganistan.

Batun kasar dai na Afghanistan na daga cikin dalilan gudanar da wannan taro na kungiyyar tsaron ta Nato.