1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyyar tsaro ta Nato ta fara samun galaba

September 13, 2006
https://p.dw.com/p/Bujb

Kungiyyar tsaro ta Nato, tace ta samu cimma nasarar kashi biyu bisa uku na yakin da take da yan kungiyyar Taliban, a kudancin kasar Afghanistan.

A cewar kakakin kungiyyar ta Nato, kungiyyar zata ci gaba da gudanar da ayyukan ta da sojojin da suke a kasa, duk kuwa da bukatar fadada rundunar sojojin da kwamandojin kungiyyar ta Nato suka yi.

Kafafen yada labaru dai sun rawaito cewa, shugabannin kungiyyar na gudanar da wani taron duba yiwuwar kara yawan dakarun sojin a kasar ta Afghanistan.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa, kwamandojin na bukatar karin soji dubu 2 da dari 5 ne, akan dubu ashirin da ake dasu, a kasar a halin yanzu.

Kafafen yada labaru sun rawaito Faraministan Biritaniya Mr Tony Blair na jaddada muhimmancin ci gaba da daukar matakan dakile fitinar yan taliban da yan Alqeda a kasar ta Afghanistan, da cewa itace hanya daya ta tabbatar da zaman lafiya a kasar.