1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kurdawa a arewacin Iraƙi sun yi maci nuna adawa majalisar dokokin Turkiya

October 18, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8E

Dubun dubatan Kurdawa a garuruwan Dahuk da Erbil dake arewacin Iraqi sun yi zanga-zangar nuna adawa da kuri´ar da majalisar dokokin Turkiya ta kada wadda ta yarda dakarun kasar su kutsa cikin Iraqi don yakar ´yan tawayen kungiyar PKK. A Dahuk masu zanga-zanga sun mikawa ofishin MDD dake garin wata takarda suna kira ga gamaiyar ta kasa da kasa da ta tsoma baki. Da farko gwamnatin Kurdawa dake arewacin Iraqi ta yi kira da a tattauna tana mai yin kashedin cewa duk wani kutse da rundunar sojin Turkiya zata yi zai haddasa rudani a Iraqi baki daya. A jiya majalisar dokokin Turkiya ta amince da daukar matakai akan ´yan tawaye amma ba ta yi karin bayani ba. Amirka da gwamnatin tsakiya a Iraqi sun yi kira ga gwamnati a birnin Ankara da kar ta aiwatar da wannan mataki. A bayan nan dai kungiyar ´yan tawayen ta yi ta amfani da sansanoninta dake arewacin Iraqi tana kai hare-hare cikin Turkiya.