1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuri'ar jin ra'ayin makomar yankin Darfur

Kamaluddeen SaniApril 11, 2016

Al’ummar yankin Darfur na Sudan ke kada kuri'ar neman jin ra’ayin kan matsayin da suka yanke ga makomar yankin duk susar lamirin da kasa da kasa suke yi ga matakin.

https://p.dw.com/p/1ITIX
Südafrika Omar al-Baschir in Johannesburg
Hoto: Reuters/S. Sibeko

Shugaban kasar Omar al-Bashir wanda kotun ICC ta ke nema ruwa a jallo a bisa laifuffukan yaki ya jaddada cewar duk da halin da ake ciki a yankin, za a cig aba da kada kuri’ar neman jin ra’ayin jama’ar a kan ko zasu hade da sauran jihohi 5 don zama yanki guda ko kuma zasu ci gaba da zama a matsayinsu.

To sai dai a hannu daya, kungiyoyin ‘yan tawaye sun kaurace wa shirin a inda suka bayyana cewar babu kamshin adalci a ciki. Ita ma kasar Amirka a nata bangaren cewar ta yi muddin kuri'ar ta gudana a karkashin jagorancin shugaba Omar al-Bashir, akwai alamar tambaya a kan sahihancin zaben.

Tun dai a shekara 2003 al’ummar yankin ke ta fafutukar samun 'yancin gashin kansu daga hannun gwamnatin Sudan a inda suke cin karo da turjiya daga hukumomin kasar.