1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuri'ar raba gardama a Kenya

November 23, 2005

Sakamakon kuri'ar raba gardamar da aka kada a Kenya ya nuna rashin gamsuwar jama'a da salon kamun ludayin shugaba Kibaki

https://p.dw.com/p/Bu3y

Shugaba Kibaki dai yayi kunnen-uwar-shegu ne da adawa mai tsananin da ya fuskanta, hatta daga wasu daga cikin ‚ya’yan jam’iyyarsa a kokarinsa na ganin lalle sai an yi wa daftarin tsarin mulkin kasar Kenya wasu ‚yan gyare-gyaren da zasu ba shi karin iko. Wannan kuwa mummunan kaye ne ga gwamnatinsa ta hadin guiwa kuma kyakkyawan ci gaba ga tsarin mulkin demokradiyya a kasar ta Kenya. A lokacin da ya dare kann karagar mulki a shekara ta 2003, shugaba Mwai Kibaki yayi wa al’umar kasar alkawarin gabatar musu da wani sabon daftarin tsarin mulki a cikin kwanaki 100 kacal. Manufarsa game da haka, kamar yadda ya nunar, shi ne kawo canji ga tsaffin tsare-tsaren da aka gada daga jam’iyyar KANU, wacce ta mulki kasar Kenya tun bayan samun ‚yancin kanta a shekarar 1963. Maganar aiwatar da canji ga daftarin tsarin mulkin ta kasance daya daga cikin shikashikan alkawururrukan da Kibaki yayi wa jama’a a yakinsa na neman zabe tare da sauran jam’iyyun hamayya dake hadin guiwa da shi a gwamnatin da aka kira wai ta hadin guiwar bakan gizo. Dukkan jam’iyyun na hadin guiwa sun yi alkawarin raba madafun iko tsakanin illahirin kabilun kasar Kenya da murkushe cin hanci a wannan kasa. Bayan nasarar zaben an nada wata hukuma da aka dora mata alhakin bitar matakan garambawul ga daftarin tsarin mulkin har tsawon shekara daya. Hukumar ta cimma daidaituwa akan kayyade cikakken ikon da shugaba ke da shi domin daga matsayin P/M da ake da niyyar nadawa. Ga alamu kuwa Kibaki bai gamsu da wannan shawara ba, kuma a sakamakon haka shi da mukarrabansa duk suka sa kafa suka yi fatali da ita. An sake bitar shawarar inda aka tankade ta ta wayi gari ba ta da wani tasiri na a zo a gani. Sabanin da aka fuskanta a game da manufar ta garambawul ta haddasa rarrabuwar hankula tsakanin wakilan majalisar ministocin gwamnatin Kibaki. Wasu ministoci bakwai suka juya wa gwamnatin baya suka canza sheka zuwa rukunin ‚yan hamayya, daidai yadda lamarin ya faru a lokacin yakin neman zaben da ya dora Kibaki kann karagar mulki. ‚Yan hamayyar sun fi kaunar ganin wani daftarin tsarin mulkin dake ba wa P/M karin ikon zartaswa. A sakamakon dagewar da ‚yan hamayyar suka yi shugaba Kibaki ya tsayar da shawarar kada kuri’ar raba gardama. Sai kuwa da aka sha fama da tashe-tashen hankula sakamakon mayar da kuri’ar raba gardamar tamkar wata manufa ta yakin neman zabe da jam’iyyun siyasar Kenya suka yi. A takaice dai sakamakon kuri’ar ta raba gardama ya bayyanarwa da gwamnatin shugaba Kibaki a fili cewar al’umar kasar ba su gamsu da salon kamun ludayinta ba, kuma ta gaza wajen cika alkawururrukan da tayi musu a yakin neman zabe. A yanzun bayan wannan mummunan kaye da ya sha ba abin da ya rage ga shugaba Kibaki illa ya ba da wata kafa ta gudanar da sabon zabe na gaba da wa’adi tun kafin ita kanta gwamnatinsa ta hadin guiwa ta rushe kwata-kwata.