1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma daidaito da 'yan tawayen Farc na Kwalambiya

Salissou Boukari
November 13, 2016

'Yan tawayen FARC na kasar Kwalambiya da bangaran gwamnatin kasar sun cimma wata sabuwar yarjejeniya a da yammacin ranar Asabar a birnin Havana na kasar Kyuba.

https://p.dw.com/p/2Sd2x
Kuba Friedensabkommen Kolumbien FARC Unterzeichnung in Havanna
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Lage

Wannan mataki dai da alama zai kawo karshen rikicin da kasar ta yi fama da shi na tsawon shekaru 52. Jim kadan bayan rattaba hannun Humberto de la Calle da ke a matsayin jagoran tattaunawar na bangaran gwamnatin ta Kwalambiya, ya nuna gamsuwarsa da suka kai ga wannan matsaya inda ya ce:

"Babban abun da muke fata dai a halin yanzu bayan cimma wannan mataki, shi ne na ganin an samu aikatawa, wanda hakan zai bada damar yafe wa juna, da samun zaman lafiya mai dorewa."

Shi ma dai daga nashi bangare babban wakilin 'yan tawayen na FARC a wannan tattaunawa Ivan Marquez, farincikin nashi ya nuna inda yake cewa:

"Sakamakon zaben raba gardama da yi yi watsi da waccan yarjejeniya ta baya, ya haifar da babban kalubale na hana aiwatar da ita, sannan da neman mayar da hannun agogo baya kan kokarin da aka yi na tsawon shekaru biyar don kai wa ga tattaunawa, amma kuma babban abun farin cikin shi ne akasarin al'ummar Kwalambiya na bukatar samun zaman lafiya."