Kwalambiya: 'Yan tawayen ELN sun sako dan majalisa
February 2, 2017Talla
Sakin tsohon dan majalisar Odin Sanchez mai shekaru 61 na daga cikin sharuddan da dama gwamnatin Kwalambiyar ta gindaya wa kungiyar tawayen kafin soma duk wata tattaunawa. Sai dai a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter Kungiyar tawayen ta ELN ta ce a yanzu ya rage ga gwamnatin kasar ta Kwalambiya da ta cika alkawarin da ta dauka na yin afuwa ga wasu kumandojinta biyu da ake tsare da su a gidan wakafi.
Kungiyar tawayen ta ELN ta ce Odin Sanchez na yanzu haka a hannun kwamitin kiyon lafiya na kungiyar, kuma nan gaba kadan za a dauke shi ta jirgi mai dirar ungulu zuwa birnin Choco na arewa maso gabashin kasar domin mika shi ga hannun hukumomi.