1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamandojin Boko Haram sun mika wuya

April 20, 2018

Wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram su 7 ciki har da mace guda, sun ajiye makamansu tare da mika wuya ga rundunar Sojin Najeriya.

https://p.dw.com/p/2wQRK
Nigeria Boko Haram Terrorist
Hoto: picture alliance/AP Photo

Wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram su 7 ciki har da mace guda, sun ajiye makamansu tare da mika wuya ga rundunar Sojin Najeriya. Su dai kwamandojin da suka tabbatar da janyewa daga kungiyar Boko Haramun din a Maiduguri babban birnin jihar Borno, sun ce sun yi hakan ne don shiga shirin afuwa da gwamnatin tarayya ta fito da shi. Kamar yadda suka shaida wa wakilin DW a yankin Al Amin Suleiman Muhammad.

Babban kwamandan Operation Lafiya Dole Manjo Janar Nicolas Rogers ya yi kira ga sauran mayakan da su ke daji, da su fito su mika wuya a shirye gwamnati ta ke ta yi musu afuwa tare da sama musu ayyukan yi.