1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin sulhu na MDD ya ɗage muhawara a kan nukiliyar Iran

March 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4F

ƙasashe biyar dake da wakilcin kujerar dundundun a kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya tare da ƙasar Jamus, sun gaza cimma matsaya a game da yadda zaá shawo kan taƙaddamar Nukiliyar ƙasar Iran. Rahotanni sun baiyana cewa ƙasashen Rasha da China sun ƙi amincewa da daukar tsauraran matakai a kan gwamnatin Iran kamar yadda kasashen yammacin turai suka bukata. Kwamitin tsaron ya dage muhawara a game da batun nukiliyar ya zuwa wani lokaci a nan gaba domin baiwa ƙasashen Faransa da Britaniya dama ta sake gabatar da wani daftari bisa laákari da hujjojin da Rasha ta bayar na kin amincewar ta. Muƙaddashin sakatare a maáikatar harkokin wajen Amurka Nicholas Burns ya baiyana amanna za su cimma matsaya guda a game da batun cikin yan kwanaki ƙalilan.