1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin sulhu ya amince da tura dakarun kare zaman lafiya zuwa Sudan.

August 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bukw

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya amince da girke dakarun kare zaman lafiya a yankin Darfur na ƙasar Sudan. Rahotanni dai sun ce za a iya tura dakaru kimanin dubu 17 zuwa yankin, idan gwamnatin Sudan ɗin ta amince da yin hakan. Kawo yanzu dai, mahukuntan birnin Khartoum na matukar adawa da wannan shirin. Kwamitin dai na son dakarun da Majalisar Ɗinkin Duniya ke niyyar girkewa a yankin na Darfur, su maye gurbin rundunar kare zaman lafiya ta ƙungiyar AU ne, wadda saboda rashin isasssun kayan aiki ta gaza hana ci gaban tashe-tashen hankulla a yankin. Tagwayen bala’o’i na yaƙi da fatara da ke addabar yankin, sun janyo mutuwar kimanin mutane dubu ɗari 3, da ƙaurar kimanin mutane miliyan biyu kuma daga matsugunansu.