1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin Sulhun MDD gaba daya ya amince da kuduri kan Lebanon

August 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bun0

A cikin daren jiya dai ne ba tare da hamaiya ba kwamitin sulhun MDD ya kada kuri´ar amincewa da kudurin da nufin kawo karshen fadan da ake gwabzawa a Lebanon. Gabanin a kada kuri´ar babban asakataren MDD Kofi Annan ya yiwa kwamitin sulhu jawabi inda a ciki ya soki lamirin membobin sa da rashin yin wani hobbasa dangane da rikicin. Kudurin yayi kira da tsagaita wuta sannan ya amince da girke dakarun MDD kimanin dubu 15 da na Lebanon dubu 15 don shaida janyewar Isra´ila daga kudancin kasar. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta ce Amirka zata marawa dakarun na MDD baya. Duk da adawar da gwamnatinsa ta nuna, FM Isra´ila Ehud Olmert yayi maraba da kudurin. A karon farko tun bayan fara wannan rikici, Olmert ya tattauna da shugaba Bush inda ya mika godiyarsa ga goyon bayan da yake samu daga Washington.