1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin Sulhun MDD ya karawa Firaminista Banny wa´adin shekara guda

November 2, 2006
https://p.dw.com/p/Budc

Kwamitin sulhun MDD gaba dayansa ya kada kuri´ar bawa FM Kodivuwa Charles Konan Banny karin iko don jagorantar wata gwamnatin wucin gadi na wa´adin shekara guda wadda zata kai ga shirya sabon zabe a kasar dake yammacin Afirka. Jakadan Peru a MDD Jorge Voto-Bernales, wanda shi ne kuma shugaban kwamitin sulhu a yanzu ya sanar da cewa membobi 15 na kwamitin sulhun sun kada kuri´ar amincewa da wani daftarin kuduri da Faransa ta gabatar wanda kuma ya samu goyon bayan kungiyar tarayyar Afirka wanda ya ya amince FM Banny da shugaba Laurent Gbagbo su ci-gaba da rike mukamansu a wani sabon wa´adi kuma na karshe da ba zai wuce watanni 12 ba.