1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamtin sulhu ya yi taron gaggawa akan halin da ake ciki a Libanon

July 14, 2006
https://p.dw.com/p/BuqX
Kwamitin sulhu na MDD ya yi wani taron gaggawa akan halin da ake ciki a Lebanon a daidai lokacin da Isra´ila ta sake kai harin bam akan filin jirgin saman birnin Beirut kwana na biyu a jere. A lokacin da yake magana a hedkwatar MDD dake birnin New York mai kula da harkokin ketare na Lebanon Nouhad Mahmoud yayi tir da hare haren sannan yayi kira da a kawo karshen farmakin da jiragen saman yakin Isra´ila ke kaiwa kasar sa. Shi kuwa jakadan Isra´ila a MDD Dan Gillermann ya kare matakin sojin na Isra´ila ne yana mai cewa ta na mayar da martani ne kai tsaye ga wani yaki da aka kaddamar a kan ta. Jakadan Amirka a MDD John Bolton ya ce Washington ta damu game da yiwuwar rugujewar demukiradiya a Lebanon da kuma aikace aikacen kungiyar Hezbollah da ka iya haddasa rashin zaman lafiya a kasar.