1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

KWANCE DAMARAN YAKI A LIBERIA.

September 8, 2004

Yau ne aka kaddamar da wani zagaye na karban makaman tsoffin mayakan liberia.

https://p.dw.com/p/Bvgd
Cibiyar horar da matasa a Liberia.
Cibiyar horar da matasa a Liberia.Hoto: AP

A yau ne Sojojin kiyaye zaman lafiya na MDd suka fara karban makamai a hannu yantawaye a wani gari dake Liberia,akarkashin wani shirin kwance damaran yaki wanda aka fara a tun a watan Afrilu,duk dacewa rashin kudi na barazana wa wannan shirin.

Ayayinda Sojojin kiyaye zaman lafiyan mdd suka cimma nasaran fara kwance damaran yakin kungiyoyin yan tawaye 3 da suka addabi wannan kasa dake yammacin Afrika a yake yaken basasa babu kakkautawa,rundunar na fuskantar matsaloli na rashin isassun kudaden gudanar da sauran rukunoni na karban makaman mayakan.

Garin Voinjama na mazama cibiyar karban makaman,tunda garin dake arewaci kuma kusa da kaniyakar Liberia da Guinea na mai zama matsugunnin yan tawaye,wadanda a bara suka tilasta tsohon madugun yan tawaye ,kuma zababben shugaba Charles Taylor,tafiya gudun hijira,wanda ficewarsa ta bude wani shafi na zaman lafiya bayan shekaru 14 ana fafatawa a liberia.

MDD wadda tun a watan Disamba ta kaddamar da shirin kwance damarar yakin,amma rashin kudi ya hanata aiwatarwa,tayi gargadin cewa kara jinkirta shrin na iya kawo tashin hankali a wadannan yankuna.Kasa da Dala milion 50 da kasashe da kungiyoyi sukayi alkawari ne ,aka samu domin aiwatar da shirin.Bugu da kari karancin kudi na kawo cikas wajen tayar da gine gine gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu sukayi alkawrin gudanarwa.

Jamaar kasar dai na kokawa da halin da Liberia ke ciki na rashin aikin yi,saboda karancin maaikatu da masanaantu.akwai kuma matsalar rashin ilimin karatu da rubutu tsakanin kananan yara ,wadanda zasu kasance manyan gobe.Akasarinsu basu ma san ko shekarunsu nawa ne ba,domin takardun haihuwansu sun bace a yake yake daya kashe sama da mutane dubu 200.

A yanzu haka dai kimanin tsoffin mayaka dubu 17,wadanda mafi yawansu mata ne da yara matasa wadanda shekarunsu basu wuce 18,suka fara makarantun koyon sanaoi,domin hadewa da sauran alumma.

Wani matashi dake karban horarwa na aikin kafinta emmanuel Saah,yayi fatan kammala horonsa a karshen watan janairun shekara mai zuwa,sai dai yace bayan sauke karatun nasa bai makomarsa ba.

Ayayinda akasarin dottijai da sukayi yakin a baya na zaman banza,kuma dan Dala 150 da aka basu saboda mika makamansu sun kare,sai bayan sun fara karban horarwa ne zasu karbi kewaye na 2 na dala 150 dinsu.

Yanzu haka dai akwai rahotanni dake nuni dacewa tsoffin mayakan saboda rashin aikinyi,na daukan abincin da mdd ke basu gudummowa ta babura daga Voinjama zuwa Guinea dake makwabtaka dasu,wanda kuma ke zama matsugunin mayakan LURD mafi girma a Liberia.Wadu kuwa sun boye makamansu a wasu jejuna dake kann iyakar kasar,akan shirin kota kwana.Abunda ake gudu yanzu shine,kada wadannan matasa su taso ba tare da wani abunyi ba,domin hakan na iya zama barazana wa zaman lafiyan kasar.

Zainab Mohammad.