1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wa'adin mulkin kabila ya kawo karshe

Yusuf Bala Nayaya
December 19, 2016

Daga wannan rana ta Litinin 19 ga watan Disamba ne Shugaba Kabila na Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango ya kamata ya sauka daga mulkin kasar saboda cikar wa'adin mulkinsa, amma kuma babu alamun hakan.

https://p.dw.com/p/2UWNe
Demokratische Republik Kongo Joseph Kabila (36406869) (Hauptbild)
Shugaban kasar Kwango Joseph KabilaHoto: Getty Images/AFP/J.D. Kannah

Babu dai sauran dama ta taka kwallon kafa a kasar Kwango har nan da makonni hudu bayan da gwamnatin Shugaba Kabila ta tsayar da wasannin lig-lig na farko da ake yi a kasar baya ga tsaida shiga shafukan sada zumunta na intanet, matakan da ke nuna fargabar da gwamnatin kasar ta shiga a fadar Fred Bauma na Kungiyar matasa 'yan fafutikar dimokaradiyya ta Lucha a Kwango.

 

Joseph Kabila Präsident Demokratische Republik Kongo
Shugaba Joseph Kabila na kasar KwangoHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

"Wannan abin bakinciki ne, abu ne mara dadi, gwamnati ta tsaida harkokin kungiyar kwallon kafa a kasa, wannan shi ke nuna yanayi na rudani da gwamnati ta samu kanta a ciki, ya na so ya tsayar da komai a kasar, a hana mutane fita ko da kuwa filin kwallon kafa ba za a iya zuwa ba, ballantana a yi maganar haduwa a kan titi, babu abin da zamu iya, babu rayuwa kenan."

Bauma dai, duk da haka ya nemi 'yan kungiyar su fita zanga-zanga a birnin Kinsasha da ma sauran kungiyoyi, muddin shugaban bai bar mulki ba. Sai dai take-taken gwamnatin kasar na sanya masa shakku. An dai tsayar da tattaunawar da ake tsakanin jam'iyyar Shugaba Kabila da gamayyar 'yan adawa kan kundin tsarin mulkin da ya hana shugaban tazarce a karo na uku har sai makon gobe.

Kongo Proteste gegen Joseph Kabila
'Yan adawan kasar Kwango lokacin wata zanga-zangaHoto: Reuters/K. Katombe

Mafi yawan 'yan kasar dai ba su goyi bayan tattaunawar da wani bangare na 'yan adawa ya yi ba kan mayar da zaben shugaban kasar ya zuwa shekara ta 2018,  Matakan da Phil Clark masanin siyasa da harkokin huldar kasa da kasa a jami'ar SOAS a London ya ce shugaban na yin wani salo ne don dawwama a kan mulki inda yake cewa:

"Dukkanin abubuwan da Shugaba Kabila ke yi tsawon watannin nan, na nuni da cewa shugaban na bin duk hanyar da ya ga zai iya bi don dawwama a kan karagar mulkin kasar. Zai ci gaba da sanya tsaiko a wajen gudanar da zabe. Dukkanin masu sharhi a kasar Kwango na ganin Shugaba Kabila a matsayin wanda zai yi kwaskwarima a kundin tsarin mulkin kasar don samun damar yin tazarce a karo na uku."

Kongo Unruhen in Goma
'Yan sandan kasar Kwango masu kwantar da tarzomaHoto: Reuters/Katombe

 

An dai jibge jami'an tsaron 'yan sanda da sojoji a sassa daban-daban na kasar ta Kwango kasancewar wa'adin shugaban zai kawo karshe da misalin karfe 12 na dare. Sai dai wata kotun kasar ta bashi damar cewa zai kasance bisa mulki har sai an yi zabe.