1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango ta dauki hankalin jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar
April 7, 2017

Jaridar Die Tageszeitung ta yi nazarin jawabin da shugaban Jamhuriyar Demukaradiyyar Kwongo Joseph Kabila ya yi wa al'ummar kasarsa bayan tsawon lokaci na jiran tsammanin warware rikicin siyasa da ake fama da shi.

https://p.dw.com/p/2arHC
Kongo Joseph Kabila
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J.Bompengo

A ranar Laraba ne dai komai ya tsaya a babban birnin kasar Kwango wato Kinshasa, a wani mataki na jiran abun da zai fito daga bakin shugaban kasar da wa'adin mulkinsa ya kare tun a ranar 19 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, amma ya ci gaba da rike madafan iko. Jaridar ta ce da ganin Joseph Kabila mai shakaru 45 da haihuwa ya gaji. Ya bude jawabin nasa ne da yin shiri na minti guda, a matsayin girmama wadanda suka rasa rayuknasu daga farkon shekara ta 2017 kawo yanzu. Daga nan ya ci gaba da tsokaci kan halin tattalin arzikin kasar da batun zaman lafiya da tashe-tashen hankula a yankin gabashin Kwangon, a jawabinsa na mintuna 40 ga al'ummar kasar.

Ya yi Allah wadarai ga wadanda ke da alhakkin rikicin gundumar Kasai, wadanda ya bayyana da kasancewa 'yan ta'adda. Daga bisani yayi alkawarin nada Firaminista, inda ya nemi 'yan adawa da su gabatar da sunayen wakilansu domin zabe. Sai dai ya ce kowa zai dauki nauyin takararsa, kuma batu ne na cikin gida banda sa bakin kasashen ketare.

Waiwaye kan kone-konen makarantu a Kenya

Kenia Universität von Nairobi Proteste
Daliban Kenya sun taba fito na fito da 'yan sandaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Azim

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung sharhi ta yi dangane da kone-konen makarantu musamman na kwana kasar Kenya tsakanin dalibai, wadanda akasrinsu ke da nasaba da rashin jin koken daliban game da matsalolinsu. Lawrence Mugo ganau ne na irin wadannan wuta da ake cunna Shekaru biyu da suka gabata. Mai shekaru 19 da haihuwa ya na kallon talabijin ne lokacin da wasu dalibai biyu suka cunna wa dakinsu wuta, lokacin da 'yan sanda suka zo kame aka hada dashi, daga bisani aka koreshi daga makarantar, duk kuwa da cewar ba shi da hannu a gobarar.

A shekara ta 2016 sama da makarantu 120 dalibai suka kone a wannan kasa da ke yankin gabashin Afirka. Akasarinsu makarantun kwana, wanda su ne kashi kashi 80 daga cikin dari na sakandaren kasar. Iyaye da dama dai sun gwammace kai yaransu makarantun kwana, musamman saboda yawan sauya wuraren aiki.

Sai dai sakamakon yawan cunna wuta a bangaren daliban a makarantun da suke da yawan yajin aiki, ya fara dasa ayar tambaya dangane da sahihancin wannan tsarin da makomar makarantun kwanan a Kenya. Ana danganta wannan matsala dai da irin tsananta wa daliban da tsarin karatun Kenyan ke dashi, ba tare da la'akari da matsalolin su daliban ba.

Äthiopien Textilindustrie - Gerd Müller
Gerd Müller ya kai ziyara wata masakar HabashaHoto: DW/B. Stehkämper

Jaridu sun tabo dangantakar Jamus da Habasha

Ziyarar da Ministan raya kasa na tarayyar Jamus ya kai Habasha domin ganin halin 'yunwa da karancin abinci da ake ciki, shi ne batu da jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi tsokaci akai. Gerd Müller ya kai ziyara yankin somali da ke cikin kasar Somaliya, domin gane wa idanunsa yadda matsalar ta yi kamari da kuma yadda ake alkinta taimakon da aka gabatar.

Gabanin ziyarar tasa dai, Amirka da Faransa sun aiki da taimako zuwa wannan yanki na somaliya da ke kan iyaka da Habasha. Tsanantar matsalar na da alaka da dumamar yanayi, wadda kasashe da dama ke da alhaki har da Jamus. A baya bayannan dai Müller ya gabatar da wani shiri na taimaka wa kasashen Afirka domin dogaro da kai, nahiyar da yace tana da damarmaki da yawa.