1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwarara yan gudun hijira daga Jamhuriya Afrika ta tsakiya zuwa Tchad

February 18, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7b

Hukumar kulla da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Dunia, ta bayyana cewar, a kalla yan gudun hijira, dubu 2 da dari 8, daga Jamhuriya Afrika ta tsakiya, su ka shiga kasar Tchad a makon da mu ke ciki.

Wannan jama´ata kauracewa rigingimun, da ke wakana a arewancin Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

Da dama da ga cikin su sun bayyana fuskantar hare hare, ko daga yan tawaye ko kuma daga wasu muitane na daban masu neman ganima.

Hukumomin kasar Tchadi, sun ce kimanin mutane 50 su ka rasa rayuka, daga ranar lahadi zuwa yanzu, a cikin tashen tashen hankulla, da su ka barke a arewanci Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

Daga farkon shekara da mu ke ciki zuwa yanzu, baki daya yan gudunhijira dubu 4 da dari 3 su ka shiga Tcadi daga makwabciyar ta Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

Idan aka gada da wannan su ke zaune tun farko yawan su zai tashi dubu 45.