1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwararar masana ilmin kiwon lafiya daga afrika zuwa ketare

Mansour Bala BelloJuly 16, 2004

Ana cigaba da fuskantar kanfa na masana ilmin kiwon lafiya a nahiyar mu ta Afrika sabili da neman Arziki a kasashen yamma

https://p.dw.com/p/Bvi2
Hoto: DW

A bisa wannan halin da ake ciki kuwa masana ilmin fannin kiwon lafiya daga hukumar kare martabar Dan Adam ce ta tabbatar da hakan a wani rahoto data bayyana a yau jummaa .A cikin rahotan dai tace irin wannan halayyar ta kwarara zuwa kasashen yamma ga likitocin kasashen nahiyar ta afrika wani koma baya ne na yaki da cutar ta kamnjamau ko ceda a nahiyar baki daya ..A cewar wannan rahoton dai ya zama wajibi a dauki mataki a tsakanin kasashe masu arzikin masaantu da kuma kasashen na afrika domin tabbatar da cewa kwalliya na biyan kudin sabulu ..Cikin wannan batun kuwa ya zama wajibi ire iren wadannan masana a tilasta masu zama a kasashen su domin cimma manufa daya .A wata kididdigar da hukumar lafiya ta mdd ta bayyana a kasashen yammacin kusa da sahara a afrika tace wadannan kasashen sun gaza samun a kalla likitoci 20 ga jammaar da suka tasamma dubu dari daya .A yayin da a binciken ya nunar da cewa kusan likitoci biyar ne ke duba lafiyar a kalla mutane sama da dubu dari a kasashen nahiyar ta afrika baki daya ..Rahotan dai na cewa a can kasar zambia ga misali batun yafi taaazzara a inda a kalla likitoci 50 ne cikin sama da dari shidda ke cikin kasar wadanda suka sami horo daga shekara ta 1978 zuwa 1999.Bugu da kari binciken wanmnan rahotan dai ya nunar da cewa a kalla ana fuskantar matsalar masu aikin jiyya a wadannan kasashe na afrika wandfa hakan ke cigaba da haifar da rudani ga fannin lafiya a yankin baki daya ..Kamar dai yarda wanda ya rubuta wannan rahoton Erik Friedmann yace da kasashen yamma da Amurka zasu hada karfi da gwamnatocin wadannan kasashe da kwalliya ta biya kudin sabulu musamman ta fannin samar da yanayi domin cimma manufar da aka sanya a gaba .A hannu guda kuma ya jaddada bukatar dake akwai na gwamnatocin kasashen su mayar da hankali kacokam ga kiwon lafiya a karkara tare da bayar da wata garabasa ga maaikatan fannin domin kara masu kwarin guiwwa na tafiyar da aikin yarda ya dace To sai dai duk da cewa ana fuskantar karancin likitoci a nahiyar ta afrika batun magance cutar kanjamau har kawo yanzu ya kasance wani kalubale ga maaikatan kiwon kafiya a duniya baki daya .MDD dai tace a kalla WADANDA KE DAUKE DA KWAYAR CUTAR TA hiv mai karya garkuwar jiki sun tasamma sama da miliyan 25 kuma yan nahiyar ta afrika sama da dubu shidda ne ke mutuwa a kowace rana a sabili da kwayar cutar Wani bincike da aka gudanar a can kasashen afrika ta kudu da Boswana cewa duk da kokarin da gwamnatotocin kasashen keyi na yaki da cutar ana cigaba da fuskan karancin masana fannin kiwon lafiya domin yaki da cutar baki daya ..To sai dai a cewar shugaban wata kungiyar dake yaki da cutar ta kanjamau dake da mazauninta a washington can kasar Amurka yace mafita daya itace bayar da kudade isassu domin yaki gadan gadan da cutar a nahiyar afrika .Domin cimma manufa kuwa dole ne a bayar da karin albashi ga maaikatan lafiya baya ga mayar da hankali ga cutar tarin fuka da cutar zazzabin cizon sauro Bugu da kari rahotan dai ya bukaci biyan diyya ga duk wata kasar data rasa ire iren wadannan masana daga kasashen da suka rike jamian domin inganta fannin lafiyar su .