1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwararowar hamada na barazana ga filayen noma

June 5, 2006
https://p.dw.com/p/BuvN
Shirin MDD na yaki da kwararowar hamada ya fid da sakamakon wani bincike da yayi wanda ke gargadi game da matsalar gurgusowar hamada a fadin duniya baki daya, musamman a yankin kudu da Sahara da kuma na kudu maso gabashin Asiya. Binciken ya kuma gano cewa a halin yanzu sauyin yanayi da yawan bukatar ruwa hade da harkar yawon bude ido sun fi yin barazana ga tsarin muhalli a yankunan hamada. Hakazalika rahoton ya ce ana amfani da ruwa fiye da kima a gonakin banruwan. Rahoton ya ce filayen noma da yanzu ke samar da abinci ga mutane miliyan dubu 2, yanzu sun fara zama hamada.