1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwararru sun Isa Nigeria

February 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8m

Kwararrun masana a fannin cutar murar tsuntsaye sun isa tarayyar Nigeria, don taimakawa wajen dakile yaduwar kwayar cutar mai sanfurin H5N1 data bulla a kasar.

A cewar wani jami´i daga hukumar lafiya ta duniya, sifetocin wadanda suka fito daga hukumar kula da abinci ta Mdd, tuni suka isa Jihohin Kaduna da Kano da kuma Filato, don fara gudanar da wannan aiki.

Tuni dai mahukuntan kasar suka bayar da bayanin cewa suna nan suna bakin kokarin su wajen ganin wannan cuta bata yi tasiri ba a wannan kasa, data fi ko wace kasa yawan al´umma a nahiyar Africa.

Kafin dai bullar wannan cuta, a yan makonnin baya kadan an fuskanci mutuwar dubbannin kaji a wasu jihohi dake arewacin kasar ta Nigeria.

Cutar ta murar tsuntsaye data bulla a shekara ta 2003, a yanzu haka tayi sanadiyyar rasuwar mutane 88 a kasashe daban daban na duniya, a hannu daya kuma da asarar miliyoyin tsuntsaye.

A wata sabuwa kuma, mahukuntan kasar Kenya sun bayar da sanarwar daina shigo da tsuntsaye irin kaji da dangogin su daga Nigeria, a matsayin rigakafi wanda hausawa kance yafi magani.