1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwarya-kwaryan cigaba wajen kai kayan agaji a Siriya

Mohammad Nasiru AwalApril 21, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana samun dan cigaba a kokarin tura kayan taimakon jin kai a yankunan da aka yi wa kofar rago a Siriya.

https://p.dw.com/p/1IaXJ
Syrien Hilfskonvoi nach Al-Rastan
Hoto: Getty Images/AFP/M. Taha

Manzon Majalisar Dinkin Duniya a Siriya Staffan de Mistura ya ce an samu wani kwarya-kwaryan cigaba wajen tura taimakon jin kai a yankunan Siriya da aka yi wa kawanya, to sai dai har yanzu gwamnatin birnin Damaskus na hana kai magunguna da sauran kayan jinya wadannan yankuna. A lokacin da yake magana da manema labarai a birnin Geneva de Mistura ya ce wannan ba abin da za a aminta da shi ba ne.

"Gaskiyar magana ita ce an samu cigaba amma ba mai yawa ba da zai sa mu ce an samu saukin lamarin. Ma'aikatan agaji na aiki ba dare ba rana don ganin kayan taimakon jin kai sun kai dukkan wuraren da ake bukata."

Majalisar Duniya Duniya da ke shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiyar Siriya a Geneva na kokarin ganin an rage halin kuncin da ake ciki a fadin Siriya bayan wani kwarya-kwaryan shirin tsagaita wuta da Rasha da Amirka suka shiga tsakani aka kulla a watan Fabrairu da ya gabata.