1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

220910 UN Reform Generaldebatte

September 24, 2010

Wasu shugabannin duniya sun buƙaci da a gudanar da sauye-sauye ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya

https://p.dw.com/p/PJYT
Taron Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New-YorkHoto: AP

Babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniyar dai ya kasance dandalin da shugabannin ƙasashen duniya daban daban ke yin amfani da shi wajen gabatar da jawabai akan batutuwa daban daban da suka shafi duniya, sai dai kuma zauren ba shi da matsayin yanke shawarar ƙarshe akan batutuwa, abinda ya sa tun a shekarun baya hatta tsohon Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Koffi Annan ya bukƙaci samar da sauye sauye ga babban zauren taron Majalisar ta yadda zai kasance mai ta'asiri sosai a harkokin tafiyar da ita.

Gabannin buɗe taron na wannan Alhamis, shugaban babban taron karo na 65 Joseph Deiss daga ƙasar Switzerland ya ce har yanzu ra'ayin jama ban sauya ba game da babban taron:

" Mutane suna ganin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya ba shi da wani ta'asiri, domin a ganin su wuri ne kawai inda mutane ke tada hayaniya su tashi, amma a zahiri bashi da wani muhimmanci".

Jamus na cikin jerin ƙasashen da ke neman sake fasalin Majalisar Ɗinkin Duniyar domin ba ta damar samun kujerar din din din a cikin Kwamitin Sulhu, inda za ta haɗe da ƙasashen Birtaniya, Faransa, Rasha da Amirka da kuma China, waɗanda dama ke da kujerun a yanzu. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wadda ke halartar taron bitar shirin bunƙasa nan da shekara ta 2015 da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shiya ta ce tana samun goyon baya da kuma ƙarfin gwiwa a ƙoƙarin da ƙasar ta ke yi na cimma burin da ta sanya a gaba, inda ta ce akwai alamar sake fasalin Majalisar a wannan jiƙon:

" Domin tabbatar da cewar an sami ci gaba a ƙoƙarin yiwa Kwamitin Sulhu gyare - gyare, abune wanda aka yi tsawon shekaru da dama ba'a yi wani abu ba akai ba." A yadda fasalin Majalisar ya ke a yanzu dai, baya ga ƙasashe biyar da ke da wakilci na din din din a Kwamitin Sulhun, akwai wasu biyar da ake sauyawa a duk shekaru biyu inda babban taron Majalisar ne ke zaɓan su. Sai dai a cewar, William Pace, darektan cibiyar kula da manufofin ƙasa da ƙasa da ke birnin New York na Amirka babban zauren Majalisar ya na da rawar da ya ke takawa:

" A shekara ta 2005, gwamnatoci sun yanke muhimman shawarwarin yin sauye - sauye ga ginshiƙan Majalisar Ɗinkin Duniya. Sun sanya batun kare haƙƙin bil'adama a matsayin ginshiƙi na ukku ga tsarin Majalisar - daura da ginshiƙanta na sulhu da zaman zaman lafiya, da kuma sha'anin bunƙasa ƙasashe."

Tuni dai Amirka ta bayyana goyon bayan ta ga sake fasalin tafiyar da lamura a Majalisar. A cewar Mrs Hillary Clinton, Sakatriyar harkokin wajen ƙasar su na maraba da batun:

" Muna bayar da cikakken goyon baya ga samar da sauye - sauye wajen gudanar da sha'anin Majalisar Ɗinkin Duniya waɗanda za su bata damar hanzarta tura isassun dakaru da jami'an 'yan sanda da ke da sahihan kayayyakin aiki da kuma irin kyawawan shugabanni da ƙwararrun da su ke buƙata."

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Yahouza Sadissou Madobi