1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwato wani yanki daga IS a Syria

March 27, 2017

Sojojin da ke yaki a Syria sun kwato wani sansanin soja da ke arewacin kasar daga ikon mayakan IS.

https://p.dw.com/p/2a00P
Syrien SDF Kämpfer vor Rakka
Hoto: picture-alliance/AP/Qasioun

Dakarun da ke da goyon bayan gwamnatin Amirka a kasar Syria sun kwace wasu sansanonin soji da ke hannun mayakan IS a arewacin kasar. Mayakan na kurdawa sun sanar jiya Lahadi cewar sansasnin sojin sama na tafkin Tabqa da ke kusa da birnin Raqqa ne suka kwace.A ‘yan kwanakin nan ne dai Amirkar ta girke daruruwan dakarun da ake wa lakabi da Syrian Democratic Forces da wasu sojojin Atilare kusa da yankin da mayakan na IS suka ja daga. A cikin watan Agustan shekara ta 2014 ne dai mayakan na IS suka karbe ikon sansanin mayakan saman na Tabqa tare da ikirarin kashe kimanin sojoji 200.

Kungiyar kare hakki ta Syrian Observatory for Human Right mai cibiya a Birtaniya, ta tabbatar da labarin. Sai dai fa wasu rahotanni na cewar fararen hula da dama na kauracewa yankin saboda fargabar da suka nuna na rashin kwanciyar hankali a kewayen nasu.