1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni

April 11, 2017

Wasannin kwallon kafa na lig da ake karawa a Turai, da ma na cin kofin hukumar kwallon kafa na kungiyoyin kasashen Afirka da ke wakana.

https://p.dw.com/p/2b2sf
Bundesliga  FC Ingolstadt 04 v SV Darmstadt 98 - Lezcano
Hoto: Reuters/M. Rehle

A wasannin kwallon kafar Jamus na Bundesliga inda sannu a hankali bayan da aka buga wasannin mako na 28 dai Kungiyar Bayern munich ke kara karfafa matsayinta na lashe gasar Bundeligar ta bana bayan da a ranar Asabar ta Lallasa Kungiyar Dortmund da ci hudu da daya a filin wasa na Alianz Arena a gaban 'yan kallo dubu 75. A yanzu dai Kungiyar ta Bayern Munich na kan tebirin gasar ta Bundesliga da maki 68, Kungiyar Leipzig na a matsayin ta biyu da maki 58 a yayin da Kungiyar Hoffenheim ke a matsayin ta uku da maki 51. A fannin yawan zura kwallaye kuma  dan wasan gaba na Kungiyar Bayern Munich Robert Lewandoski ke a sahun gaba da kwallaye 26, Pierre Aubameyang na Kungiyar Dortmund na a matsayin na biyu da kwallaye 25 sai Anthony Modeste na Kungiyar Kolon a matsayin na uku da kwallaye 23.

FC Barcelona vs. Real Madrid CF
Hoto: Getty Images/A. Caparros

A kasar Spain an buga wasannin mako na 31 na gasar la Liga inda Kungiyar Barcelona ta baras da wata babbar damar da ta samu ta darewa kan tebirin la Ligar a wannan mako, bayan da ta kusan ba zato ba tsammahani ta kwashi kashinta a hannu da ci biyu da nema a gaban Kungiyar Malaga biyo bayan Canjaras din da aka yi na ci daya da daya tsakanin Kungiyar Real madrid da kuma Kishiyarta ta Athlico Maddrid. Yanzu haka dai Kungiyar Real Madrid ke kan tebirin na la Liga da maki 72 duk da kwantan wasai daya da ke gareta. Barcelona na bi mata da maki 69.

Sai dai abin da ya fi jan hanakali a halin yanzu a gasar ta la Liga shi ne barazanar da dan wasan gaba na Kungiyar ta Barcelona Neymar yake fuskanta ta yiwuwar kasa samun  damar buga wasa a karan battar kishiyoyi ko Klasiko da za a buga makonni biyu masu zuwa tsakanin Kungiyarsa ta Barcelona da Real Madrid bayan da ya samu jan kati a wasan da suka buga a karshen mako da kungiyar Malaga. Idan dai har hukumar ladabtarwa ta gasar la ligar ta yanke hukuncin haramta masa buga wasanni biyu a nan gaba a sakamakon jan katin to kuwa sai dai ya kalli karawar klasikon a cikin 'yan kallo.

Füssballer der Hull City Ryan Mason verletzt (Schädelbruch)
Hoto: picture alliance/C. Wilson/Offside

Idan muka leka gasar Premier Ligue ta Ingila inda a karshen mako aka buga wasannin mako na 32, kungiyar Chealsea ce wacce  ta bi takwararta ta Bournemouth har gita ta lallasa ta da ci uku da daya ke ci gaba da zaman kan tebirin gasar da maki 75, Kungiyar Tottenham na a matsayin ta biyu da maki 68,a yayin da Liverpool ke bi masu da maki 68.

Har yanzu dai muna kan batun kwallon kafar amma a wannan karo a Afirka inda a karshen mako aka buga wasannin tankade da rairaye na cin kofin hukumar kwallon kafa ta Afirka wato Coupe de la Confederation ko Confederation Cup. Daga cikin wasannin 14 da aka buga Kungiyar TP Mazembe ta jamhuriyar Demokradiyyar kwango ta doke JS Kabylei ta Aljeriya da ci biyu da nema a filin wasa na birnin lumumbashi. Enugu Ranger ta Najeriya da Zesco Utd ta Zimbabye sun tashi kunna doki da ci biyu da biyu a birnin Inugu. A birnin Abija na Cote D'Ivoire  Kungiyar AS Tanda ta doke Kungiyar Platinum Stars ta  Afirka ta Kudu da ci biyu da babu.