1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni

Gazali Abdou Tasawa
April 24, 2018

Mai horas da 'yan wasan kungiyar Arsenal Arsene Wenger ya sanar da dakatar da kwatiranjinsa da kungiya a karshen kakar wasannin shekarar bana da sauran lig na kasashen Turai gami da sauran fannoni.

https://p.dw.com/p/2wZbd
Arsenal v CSKA Moscow - UEFA Europa League - Quarter Final - Fußball Trainer Wenger
Hoto: picture-alliance/empics/A. Davy

Gasar Bundesliga na Jamus a karshen mako aka buga wasannin mako na 31. Kungiyar Mönchengladbach ce ta fara tun a ranar Juma'a karya kumallo da kungiyar Wolfsburg wacce ta lallasa da ci 3-0. A ranar Assabar kungiyar Hertha berlin ta bi Frankfurt har a gida ta casata da ci 3-0, Hamburg ta yi nasar kan Freiburg da da ci daya mai ban haushi. Yaya Babba cewa da Mayern Munich wacce tun a makonni biyun da suka gabata ta tabbatar da lashe gasar ta Bundesliga ta iske Hanovre har gida ta doke ta da ci uku da banza. Stuttgart ta doke Werder Bremen da ci biyu da babu. Sai dai wasan da ya fi daukar hankali shi ne wanda aka buga a filin wasa na Red Bull Arena na Kungiyar leipzig wacce ta karbi bakuncin takwararta ta Hoffenheim. Wannan wasa wanda aka yi ruwan kwallaye kama da baki kwarya ka kawo karshe Hoffenheim na da ci biyar Leipzig na da biyu. Dan wasan gaba na Kungiyar ta Hoffenheim Mark Uth shi ne ya zura kwallon farko mintuna 12 da fara wasa.

1. Bundesliga | 1. FC Koeln v FC Schalke 04 (2:2)
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Becker

A sauran wasanni kuwa Kungiyar Dortmund ta lallasa Leverkuzen da ci hudu da babu a filin wasa na Iduna Park. Augsburg ta yi nasar kan Mayence da ci biyu da babu a yayin da Kolon ta yi kunnan doki na biyu da biyu da kungiyar Schalke 04.

A yanzu dai Kungiyar Schalke 04 ce ke a matsayin ta biyu a saman tebirin na Bundesliga, a yayin da Dortmund ke a matsayin ta uku.

A Ingila a buga wasannin mako na 35 inda Kungiyar Manchester City tuni ta tabbatar da lashe gasar ta karbi bakuncin Swansea ta ko lallasa ta da ci 5-0. Yanzu dai Manchester City din  na a saman tebirin na Primiya League da maki 90. Man united wacce ta doke Tottenham da ci biyu da daya na a matsayin ta biyu da maki 74. Liverpool na a matsayin ta uku da maki 71.

A dai gasar ta Lig na Ingila a karshen mako mai horas da 'yan wasan Kungiyar Arsenal cewa da Arsen Wenger ya sanar da cewa zai dakatar da kwatranjinsa da wannan Kungiya a karshen kakar wasannin shekarar bana. Da yake jawabi a jiya Lahadi bayan nasarar da Kungiyarsa ta yi kan West Ham da ci 4-1 ya bayyana wasu daga cikin dalillansa na dakatar da aikin nasa da Kungiyar ta Aresenal yana mai cewa:

"Bai wai dan na gaji ba ne. Amma ni ina ganin ana mutunta wannan kungiya a kasashen duniya fiye da a Ingila. Magoya bayan Kungiyar ba su nuna hadin kan da nake bukata ba kuma wannan akwai ciwo.A takaice dai ba ma gabatar da kungiyar a irin yadda ni nake so"

Brüssel Nato-Hauptquartier
Hoto: Getty Images/AFP/M. Wenger

Arsene Wenger ya lashe gasar Primiya Lig har sau uku kuma ya dauki kofin gasar kwallon kafa ta FA har sau hudu.

A kasar Spain an buga wasannin mako na 34 na gasar la Liga. Sai dai ba ta canza zane ba a saman tebirin inda Kungiyar barcelona ke kan gaba da maki 83 da kwantai na wasa daya Atletico madrid wace ta yi kunnan doki na 0-0 da Betis ta Sevilla na a matsayin ta biyu da maki 72. Real Madrid wacce ita ma ke da kwantan wasa daya na a matsayin ta uku da maki 68. A mako mai zuwa Kungiyar Barcelona na iya lashe gasar ta La Liga idan ta yi nasar a ko kuma ma kunnan doki  baya ga dama kofin sarki na kasar Spain da ta lashe a karshen mako bayan da ta lallasa kungiyar Sevilla da ci 5-0.

A sauran wasanni kuma a karshen mako an gudanar da gasar tseren kafa ta birnin London. 'A bangaren maza Eliud Kopchoge dan kasar Kenya ne ya lashe tseren a cikin awoyi biyu da mintuna hudu da sakon 17, kazalika a bangaren mata 'yan kasar ta kenya Vivian Cheruiyot ke ta zo ta farko a cikin awa biyu da mintuna 18 da kuma sakon 31.

Rafael Nadal Monte Carlo Tennis
Hoto: Getty Images/J. Finney

A fagen kwallon Tennis kuma dan wasan kasar Spain Rafael Nadal ya lashe a jiya Lahadi gasar Monte-Carlo bayan da ya doke dan wasan kasar japan Kei Nishikori. A yanzu dai Nadal ya lashe kofin gasar ta Monte Carlo so 11, kuma yanzu haka shi ne a matsayin namba one na duniyar kwallon tennis ,Roger Federer dan kasar Switzerland na  amatsayin na biyu a yayin da Alexander Zverev dan kasar Jamus ke a matsayin na uku.

Bari mu karkare shirin namu da gasar tseren babburra ta Grand Prix Des Amerique wacce ta kawo karshe a jiya Lahadi a birnin Austin na jihar texas. Marc Marquez na kasar Spain  na kamfanin Honda ne ya lashe gasar a jiya lahadi wacce ke zama nasara ta shida da ya samu a gasar  ta Grand Prix des Amerique kana ta 36 a fagen gasar tseren baburra ta duniya.