1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Laberiya: Haramtawa jami'ai fita ketere

February 6, 2017

Gwamnatin kasar Laberiya ta dauki matakin haramtawa jami'anta tafiye-tafiye zuwa kasashen waje har na tsawon kwanaki 60. Wannan dai mataki ne na dakile matsalar rashin isassun kudaden musanya da kasar ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/2X3FZ
Gambia Staatskrise ECOWAS Treffen  Ankunft Ellen Johnson
Hoto: Reuters/A. Sotunde

A karshen makon da ya gabata ne shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson Sirlef, ta bayyana kudurin hana wasu jam'ian gwamnatin kasar fita kasashen waje a wani yunkuri na inganta tattalin arziki. To sai dai a wani babi na matakin na cewa shugabar na da ikon baiwa wasu daidaiku alfarmar zuwa ziyara.

To sai dai tuni 'yan kasar ke bayyana mataki bisa yunkuri na kawo sauyi ga halin matsin tattalin arziki da take fama, dama dai tattalin arzikin kasar ta Laberiya na fuskantar koma baya tun bayan da cutar zazzabin Ebola ya barke a shekarun baya.