1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

081009 Dialog Wilfried Murad Auszeichnung

October 20, 2009

Tsohon jakadan Jamus a ƙasar Aljeriya, Willfried Murad wanda ya rungumi addinin musuluntci, shi ya samu lambar girmamawa ta wannan shekara da ake bawa musulman da suka yi fice. An ba shi wannan lambar yabo ne a Dubai.

https://p.dw.com/p/KBSP
Wilfried Murad Hofmann tsohon jakadan Jamus a Aljeriya da MarokkoHoto: picture-alliance/ dpa

Shi dai Wilfried Murad Hofmann ya kasance a jerin musulmai da suka shahar a nan Jamus. Ya wallafa littattafai da yawa sannan ya ba da gudunmawa wajen fassara ma´anonin Alkur´ani mai girma. A watan da ya gabata aka zaɓi Wilfrief Murad tsohon jakadan Jamus a biranen Aljiyes da Rabat a matsayin mutumin da ya ci lambar girmamawa ta mashahuran shugabannin addinin Musulunci na wannan shekara. Wannan lambar da ake bayarwa a Dubai, na ɗaya daga cikin lambobin girmamawa mafi daraja a duniyar Musulmi kuma ana haɗa ta da kyautar kuɗi Euro dubu 180. Lambar yabon ta bana dake zama karo na 13 a matsayin kyautar ƙasa da ƙasa kan Alkur´ani Mai Girma a Dubai, ana yi mata kallon wani muhimmin abu ga dukkan Musulmai a ƙasashen yamma da kuma waɗanda suka rungumi addinin na Musulunci. Ayyub Köhler shugaban Majalisar Tsakiya ta Musulman Jamus ya bayyana karramawar da aka yiwa Hofmann da cewa wata girmamawa ce ga ayyukan Musulmai a nan Jamus.

Daga cikin mashahuran Musulmai da suka taɓa samun wannan kyautar har da tsohon shugaban Bosniya Alija Izetbegovic. Ga shi yanzu wannan Bajamushen ya shiga jerin waɗanda suka samu wannan girmamawa ta Duniyar Musulmi a Dubai.

A cikin Firaministan Haɗɗaɗɗiyar Daular Larabawa Shaikh Mohammed Bin Rashid al-Maktum ya ayyana tsohon jakadan na Jamus a Aljeiya da Marokko a matsayin mashahurin shugaban Musulmai na wannan shekara. Hakan na matsayin daraja ayyukansa musamman ma rubuce rubucensa game da Musulunci. A lokacin da yake amsa tambaya kan dalilin da ya sa ya ci wannan lambar yabo, Wilfried Murad Hofmann mai shekaru 78 a duniya cewa yayi.

“A gaskiya ban san yadda aka yi suka zo kai na ba. To sai dai na san cewa an yi tambayoyi nan da can. Kuma ana son nunawa duniya ne cewar da akwai musulmai kuma masu yiwa addinin Musulunci aikin ƙwarai, ba kawai a ƙasashen musulmi ba, a´a har da ma ƙasashen yamma. Wato ana iya samun musulaman ƙwarai a ko-ina cikin duniya wato ko a Amirka ko a wata ƙasa ta yammacin Turai. Ina ganin wannan zaɓin da aka min na matsayin wani tabbaci da kuma amincewa da gagarumin aikin da Musulmai a ƙasashen yammacin Turai suke yiwa addinin musulunci.”

Wilfried Murad Hofmann wanda a shekarar 1980 ya musulunta, yana ɗaya daga cikin Musulmai da suka fi shahara a nan Jamus, kuma shi ne farkon wanda ya musulunta da ya samu wannan lambar yabo ta Dubai International Holy Quran Award. Ya dai mamakin samun wannan kyautar inda kwanaki biyar gabanin ya karɓi kyautar Hofmann mazaunin nan birnin Bonn, aka ba shi wannan albishir. Sarkin Dubai da kanshi ya gayyace shi zuwa bikin karɓar kyautar.

“Na samu damar ganawa da shugaban ƙasa inda muka tattauna na lokacin mai tsawo kan batutuwa da dama. Ganawar dai ta yi armashi. Mun ci abinci tare kuma mun zaga wurare da yawa musamman wuraren da ya fi sha´awa.”

Wasu jaridun ƙasashen yankin Golf sun ba da fifiko ga karramawarda aka yiwa wannan Bajamushe fiye da ziyarar da shugaban Amirka Barak Obama ya kai a wasu ƙasashen Musulman yankin.

Hofmann wanda aka haife shi a garin Aschaffenburg, da farko ya yi karatun shari´a a birnin Munich da ilimin shari´ar Amirka a makarantar koyan aikin shari´a ta Havard dake birnin Cambridge. Daga baya wato tsakanin shekarar 1961 zuwa 1994 ya yi aiki a matsayin jami´in diplomasiya, da farko ƙarƙashin ƙungiyar tsaro ta NATO a birnin Brussels sannan a ƙarshe a matsayin jakadan Jamus a Aljeriya da Marokko.

Mohammad Aman Hobohm babban aminin Hofmann, shi ma ya musulunta, ya ce kyautar da aka bawa Hofmann na nuni da irin taketakensa na kusantar addinin Musulunci. Ya ce a rayuwarsa, Hofmann ya mayar da hankali kacokan a fannin ilimin falsafa.

“Ya yi karatun jami´a a fannin ilimin falsafa a saboda haka yake ba da muhimmanci ga ilimin na falsafa. Ana dai iya ganin haka a rubuce rubucen sa. Littafin nan mai Amfani da ilimin falsafa wajen shiga musulunci shi ne littafin farko da ya wallafa. Wannan littafi na da kusancin da addinin musulunci domin ya nuna matsayinsa ga dokokin addinin na musulunci.”

An fi sanin Hofmann musamman saboda littattfai masu tarin yawa da ya wallafa kan addinin Islama da kuma lakcoci bila-adadin da ya bayar kan wannan addini a ƙasashen yammacin Turai da Amirka da kuma ƙasashen duniyar Musulmi. Ɗaya daga cikin aikinsa mafi muhimmanci shi ne gudunmawar da ya bayar wajen fassara Al-Kur´ani mai girma a shekarar 1998.

Ganin cewa wannan shi ne karo na biyu da wani Bature kuma karon farko da wanda ya musulunta ya samu kyautar ta Dubai, Majalisar Tsakiya ta Musulamna Jamus na ganin haka a matsayi wata kyakkyawar alama ta girmama ayyukan Musulmai ba kawai waɗanda suka fito ƙasashen musulmi ba a´a har ma waɗanda suka muslunta, inji Aiman Mazyek na Majalisar Musulman Jamus.

“Ana yawaita danganta shi da aikace aikacensa da batutuwan siyasa. Amma haƙiƙa shi mutum ne mai sha´awar kyawawan abubuwa musamman bisa la´akari da ɗabi´arsa, ra´ayoyinsa da kyaututtuka da kuma rubuce-rubucensa. Yana ƙoƙari don ya gano dangantaka tsakanin dokokin addinin musulunci da na ƙasashen yamma a batutuwan da suka shafi demokuraɗiyya, ´yancin ɗan Adam da ´yancin mata. A kullum ana iya gani a cikin littattafansa yadda yake ƙoƙarin nemo wuraren da sassan guda biyu suka dace da juna.”

Duk da kyaututukan da ya samu da karramawar da ake masa a ƙasashen duniyar Musulmi, Wilfried Murad Hofmann na zaman mutum mai mawuyacin hali. Kasancewar sa wani babban jami´in diplomasiyar Jamus a ma´aikatar harkokin waje da a shekarar 1980 ya fito fili ya ce ya musulunta, hakan ya zama tamkar tsokana. A cikin littfainsa mai taken “Musulunci a matsayin abin zaɓi” da ya buga a 1992, Hofmann yayi bayani kan yadda a gare shi yake ganin rayuwa ta taɓarɓare a ƙasashen yamma.

“Yana takatsantsan a rubuce-rubucensa amma a wani lokacin idan ya furta wata magana sai ka ji tamkar numfashin zai ɗauke maka. Ina ganin da gangan yake haka amma ba wai don ya nuna cewa ya fi kowa sani ba.”

Kyautar dai da Hofmann ya samu an haɗa da kuɗi Euro dubu 180, tuni kuwa ya sanar cewa zai yi amfani da wani kaso na kuɗin wajen kafa wata gidauniyar Islama ƙarƙashin Majalisar Tsakiya ta Musulman Jamus.

Mawallafa: Ulrike Hummel/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu