1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lambar yabo ta Nobel ga IAEA

October 7, 2005

An gabatar da bikin mika lambar yabo ta Nobel ga El Baradei da hukumarsa ta IAEA

https://p.dw.com/p/BvZ2
Mohammed El Baradei
Mohammed El BaradeiHoto: dpa - Bildfunk

Shi dai Muhammed El Baradei mutum ne mai sanyin zuciya da kuma halin sanin ya kamata. Amma a daya bangaren, a matsayinsa na jami’in diplomasiyyar MDD dake shugabancin hukumarta ta makamashin nukiliya, yana iya nuna taurin kai a duk lokacin da zarafi ya kama. Misali dai yadda ya tinkari gwamnatin shugaba Bush lokacin da take ikirarin cewar wai Saddam Hussein na kasar Irak na kokarin kera makaman kare dangi. A cikin gadin gaba El Baradei ya mayar da martani yana mai cewar:

Alhaki na ne in saurari ta bakin dukkan wadanda lamarin ya shafa in kuma tara hujjojinsu. Kazalika kuma alhaki na ne, daga bisani, in tsara rahoto na in kuma yi bayani dalla-dalla akan tahakikanin yadda nike kallon lamarin.

A wancan lokaci kuwa jami’in diplomasiyyar na MDD bai yi wata rufa-rufa ba, inda ya fito fili ya musunta cewar Irak na da wani shiri na kera makaman kare dangi. Wannan maganar daidai take dangane da kasar Iran, wadda Amurka ta saka ta a cikin jerin abin da ta kira wai shaidanun kasashe. Ita dai Iran ana tuhumarta da kokarin kera makaman kare dangi ne sakamakon tace uranium da take yi a yayinda ita kuma Koriya ta Arewa bata boye gaskiyar cewa tana kera makaman na kare-dangi ba. A irin wannan mawuyacin hali El Baradei ya fi sha’awar ganin an shiga tattaunawa da wadannan kasashe da yi musu tayin taimakon tattalin arziki, kamar yadda kasashen Turai ke ba da shawara. A lokacin da yake bayani akan haka El Baradei karawa yayi da cewar:

A ganina abu mafi alheri shi ne idan an ciza sai a hura, wato dai a rika rarrashi a maimakon matsin kaimi. Wannan shi ne ainifin matakin da nike amfani da shi kuma na yi imani hakan shi ne mafi alheri domin shawo kann rikicin da ake yi da Koriya ta Arewa.

A halin yanzu haka kwararrun masana na hukumar makamashi ta kasa da kasa na ba da horo ga injiniyoyi daga kasashe masu matsakaicin ci gaban masana’antu da kuma ba da shawarwarin da suka dace domin hana yaduwar wasu sinadaren makaman kare-dangi daga tsofuwar Tarayyar Soviet zuwa hannayen wasu ‚yan ta’adda. Kazalika El Baradei yayi kari wasu sabbin kudurori a yarjejeniyar hana yaduwar fasahar kera makaman kare dangi domin ba wa jami’an hukumarsa cikakken ikon bin diddigin lamarin a kasashen da ake tuhumarsu da yunkurin sarrafa wadannan miyagun makamai, kamar dai kasar Iran. Babban abin da yake sha’awar gani shi ne an kirkiro wata hanyar da zata ba da damar binciken tashoshin makamashin nukiliya domin tabbatar da cewar an yi amfani dasu ne ta hanyoyin lumana a dukkan sassa na duniya.