1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lambar yabo ta nobel

Zainab A MohammedOctober 13, 2005
https://p.dw.com/p/BwXF
Hoto: dpa

Sanannen marubucin litattafan nan na Britania Harold Pinter,ya samu lambar yabo na adabi ta Nobel.

Harold Pinter dai ya shahara a bangarori daban daban cikin litattafansa na wasanni sama da 30 daya rubuta,da kuma karuwar basirar iya magana a siyasance.

Mr Pinter dai ya fara wannan sanaa tasa ne a matsayin dan wasan kwaikwayo,inda ya rika daukan hasnkalin jamaa da basirarsa da kuma yanayin yadda tsarinsa yake.

Alkalan dai sunyi laakari da yadda pinter a daya daga wasanninsa yake kokarin kare aladarsu ,daga gurbata daga wasu bakin aladu.,da kuma inda yake nuna kamalar dan adam.

Sanannen marubucin wasan kwaikwayon wanda ya cika shekaru 75 a bana,an haife shine a kauyen Hackney dake London,mahaiofinsa kuwa ya kasance madinki ne bayahude.Kasancewarsa bayahude alokacin yana yaro ya fuskanci matsalar wariyar jinsi,wanda yayi nuni dacewa yana da tasiri wajen daukar wannan sanaa tasa ta wasannin kwaikwayo,domin amfani da baiwa da himkima da Allah ya bashi.

Alkalan wadanda suka bashi wannan lambar yabo a ranar hutu na musamman na yahudawa ,sun bayyana shi da shahara da lugga da balaga.

Ya fara rubuta wasan kwaikwayonsa a shekarata 1957,wanda yayiwa lakabi da suna The Room,.A shekara 1959 kuma shine yayi suna a shahararren wasan kwaikwayo daya rubuta mai taken The caretaker ,sai kuma The homecoming.

Duk dacewa mutun ne wanda ya iya magana baya bayyana siriin yadda yake rubuta wasannin kwaikwayonsa.

Bugu da kari Mr Pinter ya rubuta wasannin kwaikwayoi na Talabijin da suka hadar da The French Liutenants wife ,inda ya gabatar da sanannun yan wasan kwaikwayo kamar Meryl Streep da Jeremy Irons,a shekara ta 1981.

Wani wasan dayayi suna dashi shine Betrayal,inda ya gabatar da Jeremy Irons Da Kinsly.

To sai dai a yan shekaru da suka gabata Pinters d ya mayar da hankali ne kann batun siyasa.Yayi adawa matuka da kifar da gwamnatin Salvador Ayende na chile a shekara ta 1973,wanda Amurka tayiwa jagioranci,kana yasha suka lamirin salon gwamnatin marigayi tsohon shugaba Ronald Reagan na Amurka da tsohuwar primistan Britania Margaret Thatcher.

Kazalika a wannan lokaci da muke ciki ya fito fili wajen bayyana adawarsa da yakin Irakin da Amurka tayiwa jagoranci,da kuma takunkumin daya biyo baya ,da sukan lamirin turkiyya kann kurdawa,da kuma boma bomai a kosovo da azabtarwa.

A shekarata 2003 ya rubuta baiti mai warka 4 ,wanda yayiwa suna democradiyya,inda ko kadan bai nuna tsoro ko shayi ba,na tsauraran kalmomin da yayi amfani dasu.

To sai dai Mr pinter duk dacewa yayi matukar farin ciki da samun wannan lambar yabo,yace yazo masa bazata,domin bai taba tsammanin samunsa ba.

Kasancewarsa wanda ya samu wannan lanbar yabo ta bangaren rubuta adabi na wannan shekara,zai karbi kyautar Euro million 1 da digo 1,ranar 10 ga watan Disamba,ranar zagayowar mutuwar Alfred Nobel,wanda ya kafa gidauniyar bada lambar yabon ta nobel.