1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lambar yabo ta zaman lafiya

November 21, 2007

Salih Osman na Sudan ya samu lambar yabo daga Turai...

https://p.dw.com/p/C168
Salih Mahmoud OsmanHoto: Europäisches Parlament

Lauya Mai fafutukar kare hakkin jama’a a kasar Sudan Salih Mahmoud Osman,wanda ya rasa mafi yawa daga cikin iyalansa ta hanyar azabtarwa daga bangaren mayakan tawaye,ya samu lambar yabo ta kare hakkin jama’a daga kungiyar tarayyar turai.

Salih Mahmoud Osman,ya sadaukar da ransa wajen samarwa mutane tallafin magunguna da kuma adalci ta fannin sharia.Dukkannin yan majalisar turai nedai suka amince da bawa Osman wannan lambar yabo na kare hakkin jama’a,wanda ya hadar da tsabar kudi Euro dubu 50.

Mai shekaru 50 da haihuwa, wanda kuma a halin yanzu ke zama dan majalisar wakilai a gwamnatin Sudan,Osman ya samu karbuwa a bangaren turan ne sakamakon,yadda shi kadai ya samu nasara,adangane da hukunce hukuncen kisa ko kuma yanke bangaren jikin mutum,ayayinda yake aiki wa wata kungiya dake yakar azabtar da mutane a Sudan.

A yanzu haka dai yana cigaba da gudanar da kampaign na bada kariya ga wadanda aka ciwa mutunci,ta hanyar take hakkokinsu,a bangare guda kuma ,lauyan na bukatar ganin cewar an sanya fyade,a matsayin daya daga cikin laifuffukan yaki.

A dangane da wannan lambar yabo da majalisar turan ta sanar da bashi kuwa,Salih Osman ya kasa boye farin cikinsa...

“Yace nayi matukar farin ciki da samun wannan labari mai dadi.Ina ganin wannan wani abun alfahari a bangaremmu,mu masu kare hakkin jama’a aDarfur da Sudan.Wannan wata dama ce a bangaremmu na samun damar fitowa a idanun duniya ,domin bayyana halin da ake ciki a lardin darfur..”

Mayakan tawayen dai sun kashe dukkannin iyalan wannan lauya,bayan azabtar dasu kafin a kone musu gidajensu ,alokacinda shi kuma gwamnatin sudan ta daure a gidan kurkuku,na tsawon watanni 7 ,ba tare da an gurfanar dashi kan wani laifi ba,a 2004,inji sanarwar majalisar tarayyar turai.

Bayan ganawa da Osman a Sudan ne ,yan majalisaJugend Schroder daga Jamus da Jose Ribeiro Castro na Portugal ,suka gabatar da sunansa a gaban majalisar turan.

Schroder ya fadawa manema labaru cewa,idan ka hadu da Osman,bazaka taba sanin cewar shine yake aikata ire iren wadannan ayyukan ba,saboda ya kasance mutum ne mai sanyi.

Adangane da alummomin darfur kuwa Osman cewa yayi...

“Yanzu mutanen Dafur zasu sani cewar,hakki ya rataya a wuyan alummomin kasashen duniya na basu kariya,domin su samu sukunin komawa gidajensu cikin mutunci.Kuma akwai bukatar binciko dukkanin wadanda suka jefa jamaa cikin halin kakanikayi ta hanyoyi daban daban,wadanda tsarin dokarmu na cikin kasa bai bamu damar isa garesu ba,da a gurfanar dasu gaban kotun kasa da kasa mai sauraron manyan laifuffukata mdd.Munsan cewar kotun bazata iya sauraron dukkanin shariar ba,amma muna bukatar ta hukunta wadanda suka aikata manyan laifuffukan.”

Lauya Sali Osman ya bayyana cewar zaiyi amfani da kudin wajen taimakawa alummomin domin farfado musu da rayuwa...

“Ina yin nazari adangane da yin amfani da wadannan kudade , wajen yin wani abu na kyautatawa jamaa,akalla gyara wasu kanan makarantu,da Asibitoci.Wannan kyakkyawar manufa ce daga jamaar Turai,wanda ke nuni dacewar ba mu kadai ke cikin wannan wahala ba,turawa suna jinjina mana.”

Lauya Mai fafutukar kare hakkin jama’a a kasar Sudan Salih Mahmoud Osman,wanda ya rasa mafi yawa daga cikin iyalansa ta hanyar azabtarwa daga bangaren mayakan tawaye,ya samu lambar yabo ta kare hakkin jama’a daga kungiyar tarayyar turai.

Salih Mahmoud Osman,ya sadaukar da ransa wajen samarwa mutane tallafin magunguna da kuma adalci ta fannin sharia.Dukkannin yan majalisar turai nedai suka amince da bawa Osman wannan lambar yabo na kare hakkin jama’a,wanda ya hadar da tsabar kudi Euro dubu 50.

Mai shekaru 50 da haihuwa, wanda kuma a halin yanzu ke zama dan majalisar wakilai a gwamnatin Sudan,Osman ya samu karbuwa a bangaren turan ne sakamakon,yadda shi kadai ya samu nasara,adangane da hukunce hukuncen kisa ko kuma yanke bangaren jikin mutum,ayayinda yake aiki wa wata kungiya dake yakar azabtar da mutane a Sudan.

A yanzu haka dai yana cigaba da gudanar da kampaign na bada kariya ga wadanda aka ciwa mutunci,ta hanyar take hakkokinsu,a bangare guda kuma ,lauyan na bukatar ganin cewar an sanya fyade,a matsayin daya daga cikin laifuffukan yaki.

A dangane da wannan lambar yabo da majalisar turan ta sanar da bashi kuwa,Salih Osman ya kasa boye farin cikinsa...

“Yace nayi matukar farin ciki da samun wannan labari mai dadi.Ina ganin wannan wani abun alfahari a bangaremmu,mu masu kare hakkin jama’a aDarfur da Sudan.Wannan wata dama ce a bangaremmu na samun damar fitowa a idanun duniya ,domin bayyana halin da ake ciki a lardin darfur..”

Mayakan tawayen dai sun kashe dukkannin iyalan wannan lauya,bayan azabtar dasu kafin a kone musu gidajensu ,alokacinda shi kuma gwamnatin sudan ta daure a gidan kurkuku,na tsawon watanni 7 ,ba tare da an gurfanar dashi kan wani laifi ba,a 2004,inji sanarwar majalisar tarayyar turai.

Bayan ganawa da Osman a Sudan ne ,yan majalisaJugend Schroder daga Jamus da Jose Ribeiro Castro na Portugal ,suka gabatar da sunansa a gaban majalisar turan.

Schroder ya fadawa manema labaru cewa,idan ka hadu da Osman,bazaka taba sanin cewar shine yake aikata ire iren wadannan ayyukan ba,saboda ya kasance mutum ne mai sanyi.

Adangane da alummomin darfur kuwa Osman cewa yayi...

“Yanzu mutanen Dafur zasu sani cewar,hakki ya rataya a wuyan alummomin kasashen duniya na basu kariya,domin su samu sukunin komawa gidajensu cikin mutunci.Kuma akwai bukatar binciko dukkanin wadanda suka jefa jamaa cikin halin kakanikayi ta hanyoyi daban daban,wadanda tsarin dokarmu na cikin kasa bai bamu damar isa garesu ba,da a gurfanar dasu gaban kotun kasa da kasa mai sauraron manyan laifuffukata mdd.Munsan cewar kotun bazata iya sauraron dukkanin shariar ba,amma muna bukatar ta hukunta wadanda suka aikata manyan laifuffukan.”

Lauya Sali Osman ya bayyana cewar zaiyi amfani da kudin wajen taimakawa alummomin domin farfado musu da rayuwa...

“Ina yin nazari adangane da yin amfani da wadannan kudade , wajen yin wani abu na kyautatawa jamaa,akalla gyara wasu kananan makarantu,da Asibitoci.Wannan kyakkyawar manufa ce daga jamaar Turai,wanda ke nuni dacewar ba mu kadai ke cikin wannan wahala ba,turawa suna jinjina mana.”