1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

090209 Israel Araber Wahlen

Shehu, Usman/MNAFebruary 10, 2009

Yayin dake cigaba da kaɗa ƙuri'a don zaɓen ´yan majalisar dokoki wanda kuma zai kai ga samun sabon piraiminista a ƙasar Isra´ila, rikicin da take yi da Palasɗinawa yana kan gaba bisa wannan zaɓen.

https://p.dw.com/p/Gqnb
Zaɓen Isra´ilaHoto: dpa/DW

Kusan dai dukkanin Larabawa ba su da wata fata ga sabuwar gwamnatin da za'a kafa, domin a ganinsu duk Bayahude Bayahude ne. Babu irin gwamnatin da basu gani ba tun bayan yaƙin shekara ta 1967; babu gwamnatin da ta amince da dokar ba su ´yancinsu. Mussa Abu Ali wani Balarabe ne mai sana'ar aski dake zama a anguwar Beit Zafafa a kudancin birnin Ƙudus. Yana tsaye gaban shagon sa rike da almakashi, yace shi kam ba zai kaɗa ƙuri'arsa ba, biyo abinda ya faru a Gaza suma basu san makomar su ba.

"Yace koɗan ban yarda da su ba, kazalika mata ta da ɗa na da ɗiyata suma ba zasu kaɗa ƙuri'arsu ba. Kai ni ba zan yi zaɓe ba walaw Bayahude ko Balarabe ba, duk ɗaya suke. Sai yawan alƙawuran da basa cikawa. Suyi surutu, sai su yi ta mana romon baka amma babu abinda suke tsinanawa."

Masu hasashe dai sun ce haka take kusan rabin Larabawan Israela basu jefa ƙuri'arsu ba, zaɓen shekara ta 2006 shine zaɓen da yafi samun ƙarancin fitowar masu zaɓe a tarihin ƙasar. Tun lokacin takaicin da kin jinin yahudawan sai ƙaruwa yake yi. Abinda Mussa yace da ya tuna da zaɓukkan da suka gabata.

"Mussa yace muna da wata karin magana da Larabci, wato, kazo yau, kazo gobe, ba'a ga canji. A tsawon shekaru 60 babu canji da muka gani. Sai dai daga ƙarshe mu ga an ƙara muzgunawa ga Palasɗinawa. Ba ni da wani fata ga wannan zaɓen. Walau Natanyahu ne, Livni ce, ko Ehud Barak ne ya lashe zaɓen duk ɗanjuma ne da ɗan jummai. Yanayin sai cigaba da kasancewa a yadda yake"

Kusan dai batun samarwa Palasɗinawa ´yancin cin gashin kansu shine abin da yafi ɗaukar hankali a wannan zaɓen ba ga Palasɗinawa kaɗai ba harma ga masu sharhi daga ƙasasshen ƙetare. Ali Salman wani Balaraben Israela ne ya kuma bayyana hasashen sa ga wanda zai lashe zaɓen.

"Ba mamaki Natanyahu ya lashe zaɓen, ya ƙi jinin Larabawa. Yanzu haka ina mai shekaru 75 a duniya, ban ga wani alheri a cikin wannan zaɓen ba. Natanyahu ya ƙi jinin mu."

Batun samar da ƙasar Palasɗinu dai shine ke cikin zukatan dukkan Larabawa. A cikin wakilian majalisar ta Israela akwai Larabawa 13. Amma ana tsoron cewa ƙin jefa ƙuri'ar da Larabawan Israela ke nunawa tana iya maida su baya. Yawan Larabawan Israela dai ya kai kimanin miliyan ɗaya da ɗigo hudu. wato dai kusan kashi 18 cikin 100 na yawan al'ummar ƙasar ta Bani Yahudu.