1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

200209 Dialog Psychotherapie Muslime

Mohammad AwalMarch 5, 2009

Musulmi fiye da miliyan uku ne ke zaune a nan Jamus, kuma kamar sauran al´umomi su ma suna fama da matsaloli iri daban-daban, alal misali su kan yi fama da larura ta rashin lafiya wani lokacin ma har da taɓin hankali.

https://p.dw.com/p/H63w
Asibitin taɓaɓɓu a garin ErfurtHoto: picture-alliance/ ZB

To sai dai yin jiyya ta hanyar tattaunawa da likitan taɓaɓɓu game da matsalolin da shi maras lafiya ke fama da su ba tare da an ba shi magani ba na zaman wani abin ƙyama ga ɗaukacin musulmin saboda ƙarancin irin waɗannan likitoci da suka san al´adu da kuma addinan waɗannan marasa lafiya. Wai shin ana buƙatar wata jiyya ta musamman ne ga musulmi mai taɓin hankali?

A nan Jamus wasu daga cikin musulmin ƙasar da yawansu ya haura miliyan uku suna ɗari-ɗarin zuwa wajen likitoci da ba su da masaniya game da addini da kuma al´adun musulmin, musamman ga masu fama da larurar taɓin hankali. To sai dai a nan ƙasar ba safai ake samun likita musulmi da ya ƙware a fannin jiyyar masu taɓin hankali ba. Aische K. Fiel musulma ce matashiya dake fama da matsala ta fita daga cikin haiyacinta a wurin aiki da kan hanya zuwa gida ko a gida ko kuma a tsakanin ƙawayenta. Likitoci sun sha duba ta ba tare da sun gano ainihin abin da ke damunta ba. Saboda haka kamfanin inshorar lafiya ya ba da shawara da a gudanar da bincike na masu taɓin hankali a kanta.

“Na tattauna da wata ƙawata ɗaliba wadda ta ba ni shawara da in je in ga likita musulmi. Na yi aiki da wannan shawara kuma na je asibitin. Na samu ƙarfin guiwa domin bisa la´akari da wannan larura da nake fama da ita wataƙila da ban samu taimakon da nake buƙata ba daga likita da ba ma musulmi ba.”

Ganin wani musulmi likitan taɓaɓu yana da muhimmanci ga Aische wadda a kullum take rufe kanta da ɗan kwali. A halin da ake ciki yanzu tun bayan da aka fara yi mata jiyya a wasu watanni ƙalilan, Aische ta samu sauƙi daga wannan larura ta fita daga cikin haiyacinta. Yanzu dai an gano cewa wannan ciwo na ta ya samo asali ne daga wata matsala ta dangantaka. A gareta ba za ta iya tattauna wannan batu mai tsarkakiyya da wani likita wanda ba musulmi ba, domin ba su da cikakkiyar masaniya ga al´adun musulmin.

Hatta musulmin da ba sa kula da addini na da ra´ayin cewa musulmai ´yan uwansu za su fi fahimtar al´adunsu da kuma dokokin addinin. Suna fargabar cewa likitocin taɓaɓɓu waɗanda ba musulmi ba ka iya yin watsi da addininsu, inji Malika Laabda Lawi, wata musulma likitar taɓaɓɓu.

“A tunani na, musulmi marasa lafiya na fargabar cewa ba za a ba da la´akari ga al´adunsu ba. Ina ganin kafofin yaɗa labaru na taka muhimmiyar rawa a nan saboda irin labaran da suke watsawa game da addinin musulunci, wanda a lokuta da dama labarai ne na ɓatanci. Su ma majiyyatan na ganin cewa ai masu dubansu wato likitocin ´ya´yan wannan al´umma ne saboda haka salon tunanin iri ɗaya ne.”

Malika Laabda-Lawi haifaffiyar ƙasar Maroko yanzu haka dai da ita da mijinta Ibrahim Rüschoff suna tafiyar da wani asibiti a garin Rüsselsheim. Ibrahim Rüschoff ya musulunta lokacin da yake karatu a jami´a. Da shi da mai ɗakinsa sun ce bai dace ba a ce dole sai musulmi ya je wajen likita musulmi neman magani. Suka ce a likitoci musulmi musamman waɗanda suka ƙware a fannin yiwa taɓaɓɓu jiyya ba su da yawa a nan Jamus. To amma duk da haka yarda da kuma ´yar masaniya game da al´adun musulmin ya na da muhimmanci ga likitocin da ba musulmi ba. Ga Ibrahim Rüschoff batun addini bai taka wata rawa a wajen aikinsa.

“Kamar sauran likitoci masu ba da shawarwari, mu ma muna aikinmu bisa ilimin kimiyya da kuma dokokin sana´armu. To amma amincewa da juna shi ne matakin farko wanda kuma ke kawo sauƙi ga aikinmu. A gare ni ba abin damuwa ba ne idan majiyaci musulmi ya ba ni labarin rayuwarsa, zan fahimce shi domin labarin na da alaƙa da al´adunsa. Kuma wataƙila kasancewa ta musulmi na san irin tambayoyin da zan yi masa, saɓani wani wanda bai da wata masaniya game da addinin majiyacin.”

Rüschoff da Laada-Lawi sun san ƙabli da ba´adi da al´adun musulman musamman waɗanda suka shafi matsaloli a tsakanin iyali da kuma ma´aurata. Sun kuma san abubuwan da ya kamata a yiwa majiyaci da waɗanda ba su kamata ba. Da yawa daga cikin musulmai na ɗari-ɗari ga zuwa wajen likitocin masu ba da shawara saboda rashin yarda. Ɗaukacinsu sun gwammace su je wajen limamai ko kuma masu duba don neman shawara. To sai dai hakan ba shi ne mafita ba inji Malika Laabda-Lawi sannan sai ta ƙara da cewa.

“Ina ganin a tsakanin al´ummomin ƙasashen Larabawa da na Turai musamman na yankin kudancin Turai, idan ba su da lafiya sai su ce aljannu ne ko kuma wasu ƙwanƙwamai ne ke damunsu. Saboda haka ba mune matakin farko da suke zuwa wurinmu, wajen bokaye suke fara zuwa neman magani. Mu kuwa muna matsayin mataki na biyu ne idan ba a dace a wajen bokan ba.”

Manyan dalilan da ke sa musulmin zuwa wajen likitocin taɓaɓɓu shi ne matsaloli tsakaninsu da iyayen su. Yayin da iyayen ke son su ci-gaba da bin al´adun gargajiya na tun kakan kakanni, su kuwa matasan na jin kamar an takura musu ne. Sau da yawa iyayen na ba da hujja ne da dokokin addinin musulunci, to sai dai ba kullum ne ake samun wata alaƙa tsakanin ala´dun da kuma addinin ba. Laabda-Lawi ta ce matasa musulmi na neman bayani ne daga littattafan addini, intanet da abokanne kuma suna tattaunawa da iyayensu.

“Akwai ´yan Pakistan da ´yan Marokko da kuma Turkawa waɗanda ba dukkan ɓangarorin al´adunsu na gargajiya suka dace da musulunci ba. Wato kenan akwai banbanci, saboda haka matasan suke saka ayar tambaya game da shin menene musuluncin. Shi yasa suke zurfin bincike don rarrabewa tsakanin al´adun gargajiya da addini. Hakan dai na janyo rashin jituwa tsakaninsu da iyayensu. Wato ta haka matasan na yanzu suna ƙoƙarin rarrabewa tsakanin rayuwa ta addinin musulunci da kuma rayuwa a al´adance, abin da wataƙila ba ya yiwa iyayensu daɗi.”

Don magance irin wannan saɓanin bai kamata likita ya yi fatali da addinin majiyacin ko kuma ya ɗauki addinin a matsayin wani ciƙas ga sajewar baƙi a cikin ƙasa ba. To amma fargabar da yawa daga cikin musulmin kenan. Saboda haka suka fi son zuwa wajen likitoci musulmi domin suna jin an fi mutunta su wajen musulmin. Yanzu haka dai Ibrahim Rüschoff da matarsa Malika Laabdallawai sun rubuta wani littafi da zai taimakawa sauran likitoci yadda za su tinkari matsalolin da ake fuskanta da musulmi majiyata.