1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Latin Amurkac na tunawa da Mr Guevara

October 9, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8o

Al´ummomin kasashen Latin Amurka na gudanar da bukukuwan tunawa da Mr She Guevara,shekaru 40 bayan yanke masa hukuncin kisa. An dai kashe Mr Guevara ne a Bolivia a shekara ta 1967, inda yaso ya kaddamar da shirin sa na juyin juya hali.A lokacin wadannan bukukuwa, Mr Guevara, na samun yabo dangane da fice da yayi wajen kwatowa talakawa yancin su. Tuni ma shugabannin Venezuela da Bolivia suka bayyana Mr Guevara a matsayin gwarzon namiji a lokacin yana raye. Haka shima shugaba Fidel Castro na Cuba, cewa yayi Mr Guevara ya dasa danba ta gwagwarmayar neman yanci a yankin na Latin Amurka, wanda al´ummomin yankin ba za su taba mancewa dashi ba.