1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lavrov a Washington

May 10, 2017

Shugaban Amirka Donald Trump zai gana da sakataren harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, a cewar fadar White House ta Amirkar a wannan Laraba.

https://p.dw.com/p/2ckDv
Kombobild Trump Putin

Ganawar ta shugaban na Amirka Donald Trump da Sergei Lavrov, zai mayar da hankali ne kan batun samar da tuddan mun tsira a yankunan kasar Syria da ke fama da yake-yake.

Ziyarar dai na zuwa ne sa'o'i bayan sanar da sallamar shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI James Comey.

Bayanai na nunin cewa sallamar jami'in na da nasaba da bincike da ya jagoranta dangane da alakar yakin neman zaben Donald Trump da kuma Rasha.

Sai kuma yadda ya yi aiki a kan sakonnin e-mel din 'yar takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar Democrat da ta sha kayi, wato madam Hillary Clinton.