1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lavrov: Zargi na da Trump ba hujja

May 18, 2017

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya mayar da martani dangane da zargin musayar muhimman bayanan sirri tsakaninsa da shugaba Donald Trump na Amirka, yana mai bayyana hakan tamkar wani abin dariya.

https://p.dw.com/p/2dCdh
Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov
Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei LavrovHoto: Reuters/S. Karpukhin

Duk da cewar Sergei Lavrov bai bayyana abubuwan da suka tattauna da shugaba Trump din ba, Mr Lavrov ya ce bai fahimci zancen sirrin da ake kururutawa ba, musamman kan batun haramta shiga jirage da kwamfutocin Laptop saboda gudun hare-haren ta'adda.

Watanni biyu da suka gabata ne dai Amirka ta bayyana matakin haramcin shiga jirage da komfutocin gami da wasu na'urori daga kasashen yankin gabas ta tsakiya saboda dalilai na tsaro.

A cikin wannan makon ne dai jaridar Washington Post, ta yi zargin musayar bayanan sirri tsakanin shugaban Amirkan da kuma ministan harkokin wajen na Rasha, zargin da Lavrov ke cewa tamkar lokacin tsarin Komunisanci ne na baya a Rasha.