1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lebanon zata tura dakarun sojin kiyaye zaman lafiya izuwa kudancin kasar

August 16, 2006
https://p.dw.com/p/BumV

Gwamnatin Lebanon ta amince da tura ayarin dakarun soji zuwa kudancin kogin Litani,a gobe alhamis idan Allah ya kaimu.

A yayinda suke can, ana sa ran dakarun gwamnatin zasu maye guraban dakarun Izraela da suka fara janyewa.

To sai dai duk da matsin lamba daga kasashen ketare, Majalisar zartarwar Lebanon tayi watsi da batun kwance damarar yakin yan kungiyyar Hizbolla.

Hakan dai na zama daya daga cikin ka´idojin farko da aka gindaya ne a dangane da tsagaita wuta, a yakin daya dauki wata guda yana gudana tsakanin Izraela da yan Hizbollah.

A halin yanzu dai ana ci gaba da martaba kudurin sulhun da Mdd ta gabatar wanda a yau ya shiga yini na uku.

Mdd ta bayyana cewa nan da yan makonni biyu masu zuwa ne take sa ran zata tura karin dakaru kan wadanda ke da akwai a kudancin wannan kasa,wanda zai kawo ga adadin dakaru dubu 3, 500 ke nan a kudancin kasar,a karkashin jagorancin mdd.