1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libanon ta fara jibge dakarun ta a kudancin ƙasar

August 17, 2006
https://p.dw.com/p/BumT

Kwanaki 5, bayan lafawar yaƙi tsakanin Isra´ila da Hizbullahi, rundunar tsaron Labanon, ta fara jibge dakarun ta, a kudancin ƙasar, kamar dokokin Majalisar Dinkin Dunia ,su ka shinfiɗa, a yayin rataba hannu a kan yarjejeniyar tsagaita wutar.

A na sa ran, rukunin farko, na sojoji 2000, za su girka sansani yau, a wasu yankuna na kudu masu iyaka da Isra´ila.

Gwamnatin labanon, ta bayana tura sojoji dubu 15, tare da taimakon rundunar FINUL ta Majalisar Dinkin Dunia, a wannan yanki, da ya kubce ma gwamnatin tun shekara ta 1960.

Saidai, a fagen diplomatia, a na ci gaba, da tabka mahaurori a kan matakan aika rundunar ta Majalisar Dinkin Dunia, da kuma mahiman ayyukan da zata gudanar.

Ƙasashe kusan 50, za su shirya taro yau a Majalisar domin tantanawa, a kann batun.

Ƙasar France da ke sahun gaba, na ƙasashen da za su aika dakaru mafi yawa, cikin wannan runduna, ta buƙaci a haƙiƙance yaunin da ya rataya kanta, da kuma iyakokin ta.

Ministan harakokin wajen France Philips Duzte Blazy, bayan ya kai ziyara ƙasar labanaon yayi bayani kamar haka:

„Zaman lahiar da a ka samu, zai ci gabada ɗigirgire, muddun ba a cimma burin tura rundunar Labanon ba, a kudancin ƙasar, tare da amincewar baki ɗayan, membobin gwamnati.

Sannan a ɗaya hannun, dakarun Isra´ila, tare da tallafin rundunar FINUL, ta Majalisar Dinkin Dunia, su hita kwata-kwata daga“.

A nata ɓangare yau ne ƙasar Jamus ta alkawarta bada shawarwari ga Majalisar Dinkin Dunia a game batun aika rundunar shiga tsakani a kudancin Labanon.