1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

June 8, 2009

Libiya da 'yan gudun hijira a ƙasar, inda ake tsugunar da su a sansanoni masu kama da na gwale-gwale.

https://p.dw.com/p/I5hI
´Yan gudun hijira ke zanga-zanga a tsibirin Lampedusa na ItaliyaHoto: picture-alliance / dpa

A yau zamu fara ne da wani rahoto mai tsawo da jaridar Die Tageszeitung ta rubuta dangane da ƙasar Libiya ke ma'amalla da 'yan gudun hijira da kan kwarara zuwa ƙasar, inda ake tsugunar da su a sansanoni masu kama da na gwale-gwale. Jaridar ta ci gaba da cewar:

"A haƙiƙa ma dai da yawa daga cikin mahukuntan Libiya kansu ba su da wata masaniya a game da ire-iren waɗannan sansanonin da aka tanadar domin tsugunar da 'yan gudun hijirar da aka koro su daga ƙasashen Turai kamar Italiya da Malta. Amma hukumar 'yan gudun hijira ta MƊD ta ƙiyasce cewar yawansu zai kama tsakanin 25 zuwa hamsin a sassa daban-daban na Libiya. A wani sansani da jami'an kwamitin kula da 'yan gudun hijira na ƙungiyar tarayyar Turai suka kai wa ziyara a wani yanki dake da tazarar kilomita 40 a yamma da Tripoli, fadar mulkin Libiya, an tasa ƙeyar wasu 'yan gudun hijira 227 da jami'an tsaron tekun Italiya suka danƙa wa Libiya, alhali kuwa tuni wannan sansani ke da cunkoson 'yan gudun hijira sama da 600. Ire-iren wannan keta haddin ɗan-Adam tuni ya zama ruwan dare a Libiya."

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland leƙawa tayi ƙasar Zimbabwe domin tayi bitar halin da ake ciki kwanaki ɗari bayan kafa gwamnatin haɗin gambiza. Jaridar ta ce:

Robert Mugabe Präsident Zimbabwe
Shugaban Zimbabwe Robert MugabeHoto: AP

"A ɓangare guda dai an samu kyakkyawan ci gaba inda a cikin watanni ukun da suka gabata ba a fuskanci arangama ko hargitsi ba kuma ba wani labari game da take haƙƙin ɗan-Adam. A baya ga haka an mayar da kuɗaɗen musaya na ƙetare kamar dalar Amurka ko Euro ko kuma Rand na Afurka ta Kudu su zama mizanin tafiyar da al'amuran ciniki a Zimbabwe, lamarin da ya taimaka aƙalla aka samu wata 'yar daidaituwar farashin kaya, a baya ga ire-iren ci gaban da aka samu a ɓangarorin kiwon lafiya da ilimi. Amma a ɗaya ɓangaren Zimbabwe na ci gaba da fama da yawan marasa aikin yi na kimanin kashi 94%. Kazalika kashi ɗaya bisa uku na al'umar ƙasar sun dogara ne akan taimako daga ƙetare. Amma duk da haka P/M Morgan Tsivangirai na tattare da ƙwarin guiwa a game da makomar ƙasar nan gaba."

Soldaten in Mogadishu, Somalia
Mayaƙan Islama a SomaliyaHoto: AP

A can Somaliya kuwa wani sabon ci gaba aka samu inda mabiya ɗariƙu na sufiyya suka fara kutsa kansu a rikicin ƙasar bayan shekara da shekarun da suka yi suna masu keɓe kansu daga wannan rikici. A yayinda take ba da rahoto game da haka jaridar Welt am Sonntag cewa tayi:

"Bisa ga dukkannin alamu dai al'amura ne suka kai wa mabiya ɗariƙu a Somaliya iya wuya, sakamakon kai farmaki da ake yi kan maƙabartun waliyyansu da kashe-kashe na gilla akan limamansu. Hakan ta sanya suka tsayar da shawarar ɗaukar makamai domin saka ƙafar wando ɗaya da 'ya'yan ƙungiyar Al-Shabab."

Jaridar ta ambaci wani malamin ɗariƙa na Somaliya yana mai faɗi cewar sun daɗe suna masu ƙin kutsa kansu a cikin wani rikici Ya-Alla na siyasa ne ko na ƙabilanci, amma yanzu lamarin ya rikiɗe ya zama rikici na addini, a saboda haka ba zasu zauna su harɗe ƙafafuwansu ba."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal