1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: Kotu ta sake dage shari'ar Saadi Kadhafi

Salissou BoukariJuly 13, 2016

Bayan da ya shafe tsawon shakaru biyu yana jiran a yi masa shari'a, wata kotu a kasar Libiya, ta sake dage shari'ar Al-Saadi Kadhafi har zuwa ran biyu ga watan Octoba.

https://p.dw.com/p/1JNzs
Al-Saadi Gaddafi
Al-Saadi Gaddafi da masu tsaron lafiyarsaHoto: picture-alliance/dpa

Daya daga cikin jami'an da ke tsaron gidan kason birnin Tripoli inda ake tsare da Saadi Kadhafi, ya sanar cewa bisa tambayar lawyoyi masu bada kariya da basu samu damar halartar zaman kotun ba, an dage wannan shari'a har ya zuwa ran biyu ga watan Octoba mai zuwa.

Shi dai Saadi Kadhafi dan shekaru 42 da haihuwa, ana zargin shi ne da hada baki wajen hallaka masu zanga-zanga a lokacin soma zanga-zangar da ta yi sanadiyyar hanbare mahaifinsa a shekara ta 2011. A ranar shida ga watan Maris ne dai na 2014, hukumomin Jamhuriyar Nijar suka mika Saadi Kadhafi ga hannun hukumomin na Libiya.