1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libya ta fita daga jerin kasashen dake matsayin saniyar ware.

January 4, 2008
https://p.dw.com/p/Ck70

Ministan harkokin wajen Libya ya fara wata ziyara a Amirka, a karon farko da wani babban jami’in gwamnatin Libya zai ziyarci Amirka bayan kasashen biyu sun dade suna gaba da juna sanadiyar mayar da ita saniyar ware da duniya ta yi. Mohammed Abdul-Rahmana Shalgam ya yi zaman tauttauna batutuwa da dama tare da Sakatariyar harƙokin wajen Amirka Condoleeza Rice. Mai magana da yawun gwamnati Sean Mc-Cormak ya shaidawa manema labarai a birnin Washington cewar Rice ta tayar wa Shalgam da batun dokar kare haƙƙin bil’adama da ake zargin Libya da rashin biyayya da ita tare da biyan diyar harinnan na jirgin saman pasanja da ya faɗi a Lukabie.